Yanzu-yanzu: Sarkin Saudiyya ya bada umurnin bude Masallacin Madina

Yanzu-yanzu: Sarkin Saudiyya ya bada umurnin bude Masallacin Madina

Sarkin kasar Saudiyya, Malik Salman Ibn AbdulAziz ya bada umurnin bude Masallacin Manzon Allah S.A.W dake Madina fari daga ranar Lahadi, 31 ga Mayu, 2020, Saudi Gazzete ta bayyana.

Za'a fara bari mutane na shigowa amma da sharrudan kare kai daga cutar Coronavirus da ta wajabta kulle Masallaci watanni biyu yanzu.

Ma'aikatar harkokin Masallatan Harama biyu, karkashin jagorancin Sheikh Abdurrahman Sudais, ta kammala shirye-shiryen bude Malsallacin Madina da sharadin kashi 40% na mutanen da Masallacin za ta iya dauka kadai za'a amince su shiga lokaci guda.

Za'a amince Masallata su gabatar da Sallar Asuba ranar Lahadi.

Hakazalika Za'a kwashe dukkan shimfidun da ke cikin Masallacin

Yanzu-yanzu: Sarkin Saudiyya ya bada umurnin bude Masallacin Madina
Masallacin Madina
Asali: UGC

KU KARANTA: Babu wani abu mai muhimmanci da Buhari ya tsinana cikin shekaru 5 - PDP

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoto a baya cewa masarautar Saudiyya ta dakatad da shiga Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina, fari daga ranar Juma'a, 20 ga Maris ga masu khamsu-Salawati.

An yi cikin matakan da gwamnatin kasar ke dauka wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Kakakin ma'aikatar kula da lamarin Masallacin Harami da Annabi SAW dake Madina ya sanar da hakan ne ranar Juma'a.

A lokacin , mazauna cikin Masallacin da ma'aikata kadai suka sallaci sallar Asuba da Juma'a.

Yace: "Hukumomin tsaro da kiwon lafiya sun yanke shawarar hana mutane shiga cikin Masallacin Harami da na Annabi dake Madina fari daga ranar Juma'a 20 ga Maris."

"Hakan yana cikin matakan da kiyaye cigaba da yaduwar cutar Coronavirus."

A lokacin, mutane 274 kadai suka kamu da cutar kamar yadda Ma'aikatar Lafiyan kasar Saudiyya ta tabbatar.

A yanzu kuwa, mutane 81,766 suka kamu da cutar yayinda 57,013 sun samu waraka kuma 458 suka rigamu gudan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng