M.B Dongban: Buhari ya nada mace mukamin shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya

M.B Dongban: Buhari ya nada mace mukamin shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mai sharia Monica Bolna’an Dongban-Mensem a matsayin mukaddashiyar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Kakaakin shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a, 29 ga watan Mayu, inda yace nadin zai fara ne daga ranar 3 ga watan Yuni.

Garba Shehu yace shugaban kasa ya nada Dongban ne bisa tanadin sashi na 234(4) da (5) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 199, kuma nadin na tsawon watanni uku ne.

KU KARANTA: Satar N449.5m: Hukumar EFCC ta kama babban kwamandan yan bangan jahar Benuwe

M.B Dongban: Buhari ya nada mace mukamin shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya
M.B Dongban Hoto: The Nigerian Lawyer
Asali: UGC

Wannan sanarwa na nufin Mai sharia Dongban za ta cigaba da jan ragamar kotun daukaka kara a matakin riko, kamar yadda ta yi tun bayan tafiyar Mai Sharia Zainab Bulkachuwa.

A shekarar 2014 Zainab Bulkachuwa ta dare mukamin shugabar kotun daukaka kara, a zamanin Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Sharia Maryam Alooma-Mukhtar.

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin mai girma gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal a ofishinsa dake fadar gwamnatin tarayya Abuja.

Gwamna Tambuwal ya samu rakiyar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari domin ganawa da shugaban kasa a ofishinsa.

Makasudin ziyarar ita ce samun karuwar hare haren yan bindiga a jahar Sakkwato, musamman a yan kwanakin nan, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Da wannan ne shugaban kasa Buhari ya umarci rundunar Sojin Najeriya ta shiga jahar Sakkwato don tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’an jahar, da ma sauran sassan kasar.

Rahotanni sun bayyana yan bindiga sun ci karensu babu babbaka a karamar hukumar Sabon Birni na jahar Sakkwato, inda suka kashe fiye da mutane 74.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel