Alkalin Kotu ya yanke ma barawon ‘Panke’ hukuncin shekaru 2 a Kurkuku
Wata kotun kasar Czech Republic ta yanke ma wani mutumi hukuncin daurin watanni 26 a gidan yari bayan kama shi da laifin sata daga wani katafaren shago.
Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito kotun dake garin Plzen ta daure mutumin ne saboda ya saci Panke a shagon yayin da ake wahalar zaman gida saboda Korona a kasar.
KU KARANTA: Barayin mutane sun yi awon gaba da shugaban gidan talabijin na NTA
Tun a ranar 12 ga watan Maris aka sanya dokar hana fita a kasar har sai a ranar 17 ga watan Mayu aka janye dokar, don rage yaduwar cutar Korona a kasar.
A sanadiyyar dokar ta bacin ne kasar ta kirkiro tsauraran dokoki don hukunta duk wanda ya yi kokarin karya dokar zaman gidan, hatta ga wanda ya aikata karamin laifi a lokacin.
An kama mutumin ne a lokacin da yake kokarin boye panken a aljihunsa, bayan kwanaki uku kuma aka sake kama shi ya saci alawa guda 15, da ya boyesu a cikin rigarsa.
Sai dai mutumin ya bayyana ma kotu gaskiya cewa: “Ina jin yunwa ne, kuma ba ni da gida, maganan gaskiya gararamba kawai nake yi.”
A wani labarin kuma, gwamnati za ta bude manyan filayen jirgin sama a Najeriya guda hudu bayan daukan tsawon lokaci suna garkame sakamakon annobar Coronavirus.
The Nation ta ruwaito filayen jirgin saman sun hada da Malam Aminu Kano dake Kano, Murtala Muhammad dake Legas, Nnamdi Azikwe dake Abuja da na Fatakwal jahar Ribas.
A ranar 16 ga watan Maris ne gwamnati ta hana yan Najeriya zuwa kasashe 13 da suka hada da China, Amurka da Italy, kasashen da mutane fiye dubu 100 suka mutu a sanadiyyar Korona.
Kafin nan gwamnati ta rufe filayen jirgin sama a ranar 13 ga watan Maris tsawon wata daya, ta tsawaita kullewar da makonni 2, daga nan ta tsawaita shi da makonni 4 zuwa 7 ga watan Yuni.
Shugaban hukumar dake kula da sashin sufurin jirgin sama na Najeriya, NCAA, Kyaftin Musa Nuhu yace dalilin bude filayen shi ne don gudun kawo cunkoso a tsarin sufurin jirgin sama.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng