Yadda za a ci galaba kan yaki da cutar korona - Buhari

Yadda za a ci galaba kan yaki da cutar korona - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sake fayyace dalilan da za su taimakawa kasashe masu tasowa cin galaba a kan mummunan tasirin da annobar korona ta haifar.

Shugaban na Najeriya ya ce samun goyon bayan kasashe masu arziki da kungiyoyin hada-hadar kudi na duniya ga kasashe masu tasowa zai taimaka wajen cin nasara a kan annobar korona.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, shugaba Buhari a ranar Alhamis ya bukaci a yafe ma Afirka da sauran kasashe masu raunin tattalin arziki basussukan da ke kansu.

Shugaban kasar yace wannan shi ne kadai taimakon da kasashe masu arziki da hukumomi masu hada-hadar kudi za su yi wa kasashe masu rauni dawo da asarar da annobar korona ta haifar.

Buhari ya sake sabunta bukatar yafe ma kasashe masu tasowa bashi yayin da ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar bidiyo domin kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

Kimanin kasashe 50 a fadin duniya sun halarci taron wanda kasar Canada da Jamaica suka dauki nauyi yayin da babban sakataren majalisar, António Guterres ya jagoranta.

Buhari da sauran shugabanni yayin taron Majalisar Dinkin Duniya
Hakkin mallakar hoto: Garba Shehu
Buhari da sauran shugabanni yayin taron Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto: Garba Shehu
Asali: Twitter

Firaim ministan kasar Kanada, Justin Trudeau, da takwaransa na Jamaica, Andrew Holness, su ne suka daukin nauyin jagoranci tattaunawar.

Sai dai kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Buhari bai dade da yin nisa ba a jawabansa yayin da ya fuskanci matsalar rashin kyakkyawan yanayi na hanyar sadarwa da ta kawar da shi daga taron.

KARANTA KUMA: Jihohi 28 za su fuskanci ambaliyar ruwa a Najeriya

Wannan akasi na bazata da Buhari ya fuskanta ya tilastawa majalisar bai wa mai gabatar da jawabai na gaba damar dora wa daga inda ya tsaya.

Ana iya tuna cewa, makonnin da suka gabata ne Buhari ya bukaci Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya tallafawa kasashe masu tasowa wajen rage radadin da annobar korona ta jefa su a ciki.

Haka kuma shugaban kasar ya bukaci Bankin Duniya ya taimakawa kasashe masu karamin karfi wajen dakile mummunan tasirin da annobar cutar ta yi musu sanadi.

Daga cikin taimakon da shugaba Buhari ya nema akwai bukatar tsawaita lokacin dawo da rancen kudade, tallafin fasaha, rage jadawalin kudin fita a kan kayayyakin kiwon lafiya da na masarufi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel