Jihohi 28 za su fuskanci ambaliyar ruwa a Najeriya

Jihohi 28 za su fuskanci ambaliyar ruwa a Najeriya

Mahukunta a Najeriya sun yi gargadin cewa, akalla jihohi 28 ne za su fuskanci musibar ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da zai sauka a daminar bana.

A rahoton da Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NIHSA ta fitar a ranar Alhamis, ya nuna cewa akalla kananan hukumomi 102 na wasu jihohi 28 a fadin kasar za su fuskanci bala'in ambaliyar ruwa.

Jerin jihohin sun hadar Rivers, Cross River, Delta, Lagos, Ondo, Bayelsa, Sokoto, Kogi, Niger, Kaduna, Gombe, Adamawa, Benue da Abuja.

Saura garuruwa sun hadar da; Nasarawa, Delta, Oyo, Ogun, Osun, Ekiti, Ebonyi, Edo, Abia, Anambra, Imo, Borno, Kano da Kebbi.

NIHSA ta fitar da sakamakon hasashen da ta yi dangane da daminar bana kuma ta gabatar da rahoto cikin birnin Abuja.

Ministan Ruwa, Suleiman Adamu, ya lura cewa an yi hasashen ne domin daukan izina ta musibar da ambaliyar ruwa ta haddasa a kasar a shekarar 2012.

Ministan Ruwa; Suleiman Adamu
Ministan Ruwa; Suleiman Adamu
Asali: Depositphotos

Ya ce makasudin hasashen shine gabatar da yanayin yiwuwar ambaliyar a wannan shekara da kuma ankarar da al'umma, musamman mazauna yankunan da ke da hatsarin fuskantar ambaliyar domin rage tasirin da za ta haifar.

KARANTA KUMA: Ranar 17 ga watan Yuni za a dawo gasar Firimiya ta Ingila

Ya ce ambaliyar ruwa na daya daga cikin bala'o'in da suka saba aukuwa a Najeriya tare da haifar da mummunan tasiri a kan talakawa da marasa galihu da ba za su iya rayuwa ba sai a gabar kogi.

Sai dai ya ce koda yake hasashen ya nuna cewa ambaliyar bana ba za ta yi tsanani ba kamar shekarun baya.

Ya nuna cewar mma yana da muhimmanci ga dukkan masu ruwa da tsaki su gudanar da wani gangami na wayar da kan jama'a domin su kasance cikin shiri.

Ya kara da cewa, "yana da muhimmanci a san cewa lokacin ambaliyar ruwa ya tunkaro baya ga annobar cutar korona da ake fuskanta, lamarin da ya ce barazana biyu kenan a lokaci guda."

Ministan ya ce kamar yadda a koda yaushe, ambaliyar ruwa ta na da alaka da hatsarin kamuwa da cututtuka

Ya ce hakan na faruwa ne a yayin da 'yan gudun hijira suka cure a wurin neman mafaka, lamarin da ya ce yana da muhimmanci ga duk masu ruwa da tsaki su daura damara tun a yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng