Yanzu-yanzu: Babu sauran mai cutar Coronavirus a jihar Kebbi - Gwamnatin jihar

Yanzu-yanzu: Babu sauran mai cutar Coronavirus a jihar Kebbi - Gwamnatin jihar

Kwamitin kar ta kwanan yakar cutar COVID-19 na jihar Kebbi, a ranar Alhamis ya sallami mutum biyu na karshe masu dauke da cutar ta Coronavirus a jihar.

Shugaban kwamitin wanda shine kwamishanan lafiyan jihar, Jafar Muhammad, ya bayyana hakan ne a cibiyar killace masu cutar dake Asibitin KMC dake Kalgo, jihar Kebbi.

Yace: "Mutane biyu masu cutar Coronavirus da suka rage a cibiyar killacewarmu dake asibitin KBC Kalgo sun samu sallama yau, Alhamis, 28/5/2020."

Muhammad ya kara da cewa an sallami mutane biyun da suka rage ne bayan sakamakon gwaji daban-daban ya nuna cewa sun barranta daga cutar.

A cewarsa, "Saboda haka, sun samu yanci kuma zasu cigaba da rayuwarsu cikin jama'a bayan sakamakon gwajinsu ya nuna cewa basu dauke da cutar bayan makonni biyu a cibiyar killacewa."

Kwamishanan wanda yake cike da farin ciki ya karkare maganarsa da cewa yanzu jihar ba ta da ko da mutum daya mai dauke da cutar Korona.

KU KARANTA: Ta kan Sallar Idi, gwamna ya sallami Limamai uku

Yanzu-yanzu: Babu sauran mai cutar Coronavirus a jihar Kebbi - Gwamnatin jihar
Gwamnan jihar Kebbi
Asali: UGC

A ranan Litnin, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Zamfara, Muhammadu Bello Matawalle ya ce masu fama da cutar Coronavirus takwas kadai suka rage a jiharsa da aka killace a cibiyar killacewa.

Matawalle ya bayyana hakan jiya a wani taro a garin Maradun inda ya je more hutun bikin karamar Sallah (Eidul Fitr).

Gwamnan ya yabawa ma'aikatan kiwon lafiyan jihar bisa nasarar da suka samu wajen bibiyar wadanda suka kamu da cutar tare da jinyarsu.

Ya bayyana farin cikin cewa yanzu babu sabon mai dauke da cutar a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel