COVID-19: Karin mutum 182 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 8915

COVID-19: Karin mutum 182 sun kamu da korona a Najeriya, jimilla 8915

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 182 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.27 na daren ranar Alhamis, 28 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 182 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-111

FCT-16

Akwa Ibom-10

Oyo-8

Kaduna-6

Delta-6

Rivers-5

Ogun-4

Ebonyi-4

Kano-3

Plateau-2

Gombe-2

Kebbi-1

Kwara-2

Bauchi-1

Borno-1

DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan 'yan bindiga a Zamfara

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Alhamis 28 ga watan Mayun 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 8915.

An sallami mutum 2592 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 259.

A wani labarin daban, kun ji cewa Gwamnatin jihar Kogi ta ce babu wani mahaluki da ya kamu da cutar COVID-19 da aka fi sani da korona a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa da kwamishinan Lafiya na jihar, Saka Haruna Audu, ya fitar a ranar Laraba ya ce jihar tana da kayan gwaji kuma ta yi gwaje-gwaje masu dimbin yawa kuma duk sun nuna babu mai cutar.

Wannan matsayar ta ci karo da ta Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya, NCDC. Hukumar ta ce mutane biyu sun kamu da COVID-19 a jihar.

A cikin sanarwar, Audu ya ce jihar ba za ta amince da wani “labarin kanzon kurege na bullar COVID-19 a jihar ba ”.

Ya ce, "A halin yanzu babu COVID-19 a jihar Kogi. Muna da kayayyakin gwaji isassu kuma munyi darurruwan gwaje gwaje kuma sakamakon ya nuna babu mai cutar."

"Kamar yadda muka fadi a baya, ba za mu amince da wata karya na ikirarin bullar COVID-19 ba shi yasa ba zamu amince da duk wata gwaji da wani dan Kogi ya yi a wani wuri da ba jihar mu ba kuma ba a tuntube mu ba.

"Ba za mu amince da duk wani yunkurin tilasta mana bullar COVID-19 a jihar mu ba."

"A shirye muke mu kula da lafiyar mutanen jihar mu kuma ba mu da shaawar yin siyasa da batun lafiyarsu," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel