Sokoto: Buhari ya yi martani mai zafi a kan kisan mutum 50
A ranakun Lahadi da Laraba ne 'yan bindiga suka kutsa karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto inda suka halaka rayuka sama da 50 yayin da suke bikin shagalin Idin karamar sallah.
Mazauna garin sun tabbatar da cewa maharan ranar Lahadi ne suka sake dawowa a sa'o'in farko na ranar Laraba, bayan Gwamna Aminu Tambuwal ya ziyarci yankin don ta'aziyya.
Harin farko na ranar Lahadi ya faru ne bayan rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta fitar da takarda mai tabbatar wa da mazauna jihar tsaro mai nagarta yayin da suke shagalin bikin sallar.
"Kwamishinan 'yan sandan jihar Sokoto na tabbatar wa da jama'a cewa rundunarsa shirye take wajen bada isasshen tsaro ga rayukansu da kadarorinsu yayin bikin sallah," Muhammad Sadiq, kakakin rundunar 'yan sandan ya tabbatar.
Wasu mazauna yankin sun tabbatar wa da jaridar Premium Times cewa sama da 'yan bindiga 100 ne suka tsinkayi garin a kan babura tare da yin barna ba tare da wani kalubale ba.
DUBA WANNAN: Kalli bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan 'yan bindiga a Zamfara
Yankunan da abun ya shafa sun hada da Kuzari, Katumi, Masawa da Dan Aduwa. Dukkan yankunan na da nisan kilomita kalilan tsakaninsu da garin Sabon Birni.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani mai zafi game da al'amarin a yau Alhamis, ya ce wannan babban abun alhini ne.
"A yayin da duniya da Najeriya ke fama da annobar Coronavirus, abun takaici ne yadda 'yan bindiga suka ci gaba da kai hari wasu yankuna na kasar nan tare da kashe jama'a," kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya sanar a wata takarda da ya fitar.
"Ba za mu yi watsi da ku ba saboda a shirye muke don kawo makasan talakawa tare da murkushe su."
Kamar yadda takardar ta bayyana, "Shugaban kasa ya tabbatar da cewa an kaddamar da wata sabuwar runduna mai suna " Operation Accord" a yankin don hana 'yan bindigar sakat a yankin.
"Wannan rundunar na da kudirin kawo karshen 'yan bindiga da hana su numfasawa a yankin kwata-kwata."
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa a shirye take wajen bada kariya a kan wannan kisan kiyashin da ake wa jama'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng