Da duminsa: Ta kan Sallar Idi, gwamna ya sallami Limamai uku

Da duminsa: Ta kan Sallar Idi, gwamna ya sallami Limamai uku

Sakamakon saba sharrudan gudanar da Sallar Idi da Huduba da gwamnatin jiha ta gindaya a ranar Sallah, gwamnatin jihar Neja ta baiwa Limamai uku takardar sallama.

Gwamnatin jihar ta bada umurni ta kwamitin kar ta kwana kan yaki da Coronavirus cewa a gudanar da Sallar Idi a wasu zababbun Masallatai ba a filin Idi ba.

Hakazalika an hana mata da yara halartan Sallar.

Gwamnatin ta bada umurnin ne bisa ga shawarar kwamitin da ma'akatar harkokin addinai a jihar ta nada domin duba abubuwan da Malaman addini ke yi.

Kwamitin ta kama wadannan Limamai da laifi.

Limaman da aka sallama sune Alhaji Abdullahi Ndakogi na Masallacin Batagi dake masarautar Bida; Malam Mohammed Idris na Masallacin rukunin gidajen Bosso dake Minna; sannan Awwal Yusuf na Kontagora.

KU KARANTA: Yan Boko Haram 188, yan bindiga 411 muka kashe a watan Mayu - Hedkwatar Sojin Najeriya

A jawabin da Malam Mustafa Tauheed, hadimin dirakta janar na ma'aikatar harkokin addinai, Dakta Umar Farouq, ya saki, an tsige Ndakogi matsayin Imam Ratibi na Batagi kuma an maye gurbinsa.

Hakazalika, An sauke Malam Idris daga limancin Masallacin Bosso ne saboda ya saba dokar jihar na gudanar da Sallar Tahajjud da Tarawihi.

Shi kuwa Malam Yusuf na Kontagora, an kama shi ne da laifin yin kalaman suka da tunzura mutane a hudubar Idin da ya gudanar.

An dakatad da shi daga wa'azi a jihar na tsawon shekara daya

Bugu da kari an umurceshi ya rubuta wasikar alkawari cewa zai zauna lafiya da gwamnati kuma zai bada hakuri.

Za ku tuna cewa Gwamnatin jihar Neja, Adamawa, Bauchi, Nasarawa, da Kano sun amince al'ummar jihar su gudanar da Sallar Idi amma da wasu sharruda.

Daga cikin sharrudan shine kada a gudanar da Sallah a filin Idi, sannan ayi amfani da takunkumin fuska kuma a bada tazara.

Amma yawancin Masallatan da aka gudanar da Sallan sun sabawa sharrudan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel