Babban sufetan Yansandan Najeriya ya yi ma kwamishinonin jahohi garambawul

Babban sufetan Yansandan Najeriya ya yi ma kwamishinonin jahohi garambawul

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bada umarnin dauke kwamishinonin Yansandan jahar Edo, Ondo da Oyo.

Punch ta ruwaito baya ga kwamishinonin jahohi uku, sufetan ya bada umarnin sauya ma wasu kwamishinoni guda takwas wuraren aiki, kamar yadda shelkwatar Yansanda ta sanar.

KU KARANTA: Kowa da ranarsa: Tubabbun yan bindiga sun kwato mutane 12 daga hannun yan bindigan Zamfara

Kakaakin Yansandan Najeriya, DCP Frank Mba ne ya sanar da cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis,28 ga watan Mayu, inda yace:

“Sufeta janar na Yansandan Najeriya ya bada umarnin nada kwamshinonin Yansanda kamar haka; CP Johnson Babatunde Kokumo zuwa jahar Edo, CP Undie J Adie zuwa jahar Bauchi, CP Lawal Jimeta Tanko zuwa jahar Bauchi.

Babban sufetan Yansandan Najeriya ya yi ma kwamishinonin jahohi garambawul
Babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammad Adamu Hoto: Twitter
Asali: UGC

“CP Philip Sule Maku zuwa jahar Ebonyi, CP Ahmad Maikudi Shehu zuwa jahar Gombe, CP Bolaji Amidu Salami zuwa jahar Ondo, CP Joe Nwachukwu Enwonwu zuwa jahar Oyo, CP Evelyn Peterside zuwa tashar jirgin ruwa ta yankin gabashin Najeriya.

“CP Okon Etim zuwa sashin binciken bamabamai, CP Bello Maikwashi zuwa sashin jiragen sama sai CP Olukola Tahiru Shina zuwa sashin yaki da zamba da yan damfara.” Inji Mba.

IG ya shawarci sabbin kwamshinonin su tabbata sun kare aukuwar miyagun laifuka, tsaron al’umma da kuma saura manyan laifuka.

Haka zalika ya nemi jama’a su baiwa sabbin kwamishinonin hadin kai wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A wani labari, wasu ayarin tubabbun yan bindiga a jhar Zamfara sun ceto kimanin mutane 12 da wasu miyagun yan bindiga suka sace su, kuma tuni sun mika su hannun Yansanda.

Punch ta ruwaito kakaakin rundunar Yansandan jahar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka, ina yace a ranar 27 ga watan Mayu ne tubabbun yan bindigan suka nuna bajinta.

“Kwamitin zaman lafiya na jahar Zamfara tare da hadin gwiwar tubabbun yan bindiga sun ceto mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane. Kimanin makonni biyu da suka gabata aka yi garkuwa da mutane.

“Amma Allah Ya kubutar da su ta hannun tubabbun yan bindiga da suka kai harin kwantan bauna kan miyagun yan bindigan da suka yi garkuwa da mutanen.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel