Matashi ya dambace da mahaifinsa saboda ya hana shi kudin abinci (Bidiyo)

Matashi ya dambace da mahaifinsa saboda ya hana shi kudin abinci (Bidiyo)

Wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da wani yaro ke dambe da mahaifinsa a jihar Abia.

A cikin bidiyon, an hasko wani yaro mai suna Abuchi yana dambe da mahaifinsa a kofar gidansu a bainar jamaa.

An ji murya daga cikin bidiyon na yi wa yaron gargadi a lokacin da ya ke cigaba da dambe da mahaifinsa.

Wani da ke kallon abinda ke faruwa ya yi kokarin shiga tsakani domin ya raba fadan da ke tsakanin mahaifin da dansa.

Daga bisani ya tura matashin da mahaifinsa cikin gidansu.

A cewar rahotani, matashin yana fushi da mahaifinsa ne domin ya hana shi kudin cin abinci tun lokacin da aka kafa dokar kulle a jiharsu sakamakon bullar annobar coronavirus.

DUBA WANNAN: Kungiya ta siya wa gwamnan APC fom din takara

Ga bidiyon a kasa kamar yadda LIB ta ruwaito labarin.

A wani rahoton, kun ji cewa diraktan kungiyar rajin kare hakkin Musulmi (MURIC), Ishaq Akintola ya ce gwamnoni da suka bari aka yi sallar Idi a jam'i sun yi babban laifiin da ya kamata a tsige su daga kujerunsu.

A ranar Lahadi, an yi sallar Idi a Jam'i a jihohi masu tarin yawa na fadin kasar nan. Wannan kuwa take doka ce tare da rashin biyayya ga umarnin kwamitin yaki da cutar korona na kasa baki daya.

An yi sallolin ne a cunkushe ba tare da saka takunkumin fuska ba duk da cincirindon jama'a. A misali, jihar Kano wacce a halin yanzu take a ta biyu a yawan masu cutar korona a kasar nan, ta yi sallar idi da cincirindon mutane.

A wata takarda da kungiyar ta fitar, Akintola ya ce abin da gwamnoni suka yi ya sha bambam da umarni gwamnatin tarayya, Jama'atu Nasril Islam da kuma majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci ta Najeriya.

Ya bukaci 'yan majalisar jihohin da abun ya shafa da su yi abinda ya dace akan abinda gwamnonin suka yi don laifin ya cancanci tsigewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel