COVID:19: An rufe hedkwatan NDDC bayan mutuwar darakta a hukumar

COVID:19: An rufe hedkwatan NDDC bayan mutuwar darakta a hukumar

Daraktan hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta (NDDC) ta gaggauta garkame ofishinta na makonni biyu bayan mutuwar mukaddashin daraktan kudi, Ibanga Bassey Etang.

Akwai zaton da ake yi na cewa mukaddashin daraktan hukumar ya rasu ne sakamakon kamuwa da annobar korona. Ta fitar da umarnin rufe ofishin na makonni biyu tak.

Silas Anyawu, wanda ya sa hannu a kan takardar a madadin hukumar, ya rubuta: "Ina umartar dukkan ma'aikatan hukumar NDDC da su dakata da aiki don rufe ofishin da za a yi na makonni biyu daga ranar 28 ga watan Mayun 2020.

"Hakazalika, dukkan ayyukan hukumar ya tsaya cak har zuwa lokacin da za ta dawo aiki.

"Ana shawartar dukkan ma'aikata da su tabbatar da cewa sun kashe kayayyakin wuta da ke ofishinsu kafin tafiya hutun.

"Da wannan takardar ake umartar shugaban fannin tsaron hukumar da ya fitar da tsare-tsaren tsaro na hukumar yayin da ake umartar feshin ofishin kafin a dawo.

NDDC ta garkame hedwaktar ta bayan mutuwar daraktan hukumar
NDDC ta garkame hedwaktar ta bayan mutuwar daraktan hukumar. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Korona: Najeriya ta samu karin mutum 389, yanzu mutum 8733 suka kamu

"Ana ci gaba da umartar ma'aikatan hukumar da su killace kansu na makonni biyu yayin da ake jiran wani umarni daga hukumar."

Mutuwar daraktan na zuwa ne bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin miko bayanin kudin da suka shiga tare da fita a hukumar.

A watan Oktoba na 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya binciki al'amuran hukumar tun daga shekarar 2001 zuwa 2019.

A ranar Laraba, majalisar dattijan kasar nan ta kafa kwamitin wucin-gadi na bincikar kwamitin rikon kwarya na NDDC a kan zarginsu da aka yi da almundahanar kudi har naira biliyan 40.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin samanta na rundunar Operation Hadarin Daji sun ragargaza ma'adanar makamai tare da kashe a kalla 'yan bindiga 30 a samamen da ta kai ta jiragen yaki.

Dakarun sun kai samamen ne a ranar Talata zuwa dajin Doumborou da ke jihar Zamfara.

John Enenche, shugaban fannin yada labarai na rundunar, a wata takarda da ya fitar ya ce, rundunar ta kai harin ne bayan bayanan sirri da ta samu.

Bayanan sun nuna cewa akwai wata ginin jinka da ke dajin wacce 'yan bindigar ke amfani da ita wajen adana makamai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel