Gaskiya ta yi halinta: Kalli wasu masoya biyu da suka gano yan uwan jini ne su gab da aurensu

Gaskiya ta yi halinta: Kalli wasu masoya biyu da suka gano yan uwan jini ne su gab da aurensu

Wasu masoya biyu yan kasar Kenya sun gano cewa ashe babansu daya bayan sun dauki tsawon lokaci suna soyayya da juna, har an sanya musu ranar aure.

Jaridar The Nation ta ruwaito a bisa dole ta sa John Njoroge ya kashe aurensa da Rose Wanjiku kasantuwar sun gano yan uwan juna ne su na jini a yayin da ya bayyana daga iyayensa.

KU KARANTA: Mutane 5 sun mutu, 5 sun jikkata a wani hadari da ya faru a jahar Kano

Da yake bayar da lamarin mawuyacin halin da ya shiga, Njoroge ya bayyana cewa Wanjiku kanwarsa ce, diyar matar babansa ta biyu, kamar yadda ya shaida ma Kameme TV.

“Bayan na kai ta gidan mu don na nuna ta ga iyaye na, shi ne aka fada min cewa mahaifina yana da wata mata, kuma ita ta haifi Wanjiku, don haka yan uwan jini ne mu.” Inji shi.

Gaskiya ta yi halinta: Kalli wasu masoya biyu da suka gano yan uwan jini ne su gab da aurensu
Masoyan Hoto: The Nation
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana an fara soyayya tsakanin Njoroge da Wanjiku ne bayan ta ba shi sautin takalma, kuma ya kawo mata har gida, daga nan suka saba, har soyayya ta kullu a tsakaninsu.

A sanadiyyar wannan hatsarin, Wanjiku ta bayyana shakkun sake yin soyayya, don gudun kada ta kara fadawa soyayya da wani dan uwanta da bata sani ba.

“Ba zan iya kara soyayya da wani mutum ba, saboda ina tsoron shi ma zai iya kasancewa dan uwana ne.” inji ta.

A wani labari kuma, Shugaban kasar Kenya, Mista Uhuru Kenyatta ya gargadi ƴaƴansa musamman maza daga cikinsu dangane da yi ma dokar da ya sanya ta hana fita karan tsaye.

Shugaba Kenyatta ya sanya dokar hana fita a kasar ne domin dakile yaduwar annobar Coronavirus, inda a yanzu haka cutar ta fi kamari a birnin Mombassa ta kasar.

Shugaba Kenyatta ya bayyana ma jama’an kasar cewa a kwanakin baya yaransa biyu sun karya wannan doka, inda suka yi takanas ta Kano zuwa birnin Mombassa don holewa.

Haka zalika shugaban ya nuna damuwarsa da yadda yaran nasa suka jefa rayuwar mahaifiyarsa, Ngina Kenyatta cikin hadarin kamuwa da cutar saboda a wurin ta suka sauka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng