Buhari: Gwamnoni uku sun gana da Malami a kan bawa majalisu da bangaren Shari'a 'yanci

Buhari: Gwamnoni uku sun gana da Malami a kan bawa majalisu da bangaren Shari'a 'yanci

- Shugaba Buhari ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya bashi wajen bawa majalisun jihohi da bangaren shari'a 'yancin cin gashin kai a harkar kudi

- Gwamnonin sun ce sabuwar dokar za ta yi wa sha'anin gudanar da mulki a matakin jihohi babbar illa

- Kungiyar gwamnonin ta kafa kwamitin mutum uku da zai cigaba da tuntubar ministan shari'a na kasa, Abubakar Malami

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun amince da shawarar tuntubar ministan shari'a, Abubakar Malami, domin tattaunawa a kan illolin da ke tattare da dokar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya zartar.

A cewar gwamnonin, sabuwar dokar da akewa lakadabi da 'Executive Order 10, 2020' za ta kawo nakasu a harkokin gudanar da gwamnati a matakin jihohi.

A saboda haka, kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta kafa kwamitin mutane uku da zai cigaba da ganawa da Malami a kan batun.

Kwamitin ya hada da gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Simon Lalong na jihar Filato, da Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NGF, Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti, ya fitar ranar Alhamis bayan kammala taron da gwamnoni su ka gudanar ta hanyar fasahar zamani.

Buhari: Gwamnoni uku sun gana da Malami a kan bawa majalisu da bangaren Shari'a 'yanci
Abubakar Malami
Asali: Twitter

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya saka hannu a kan dokar bawa bangaren shari'a da majalisun jihohi ikon cin gashin kansu a harkokin kudi.

A cewar wani jawabi mai dauke da sa hannun kakakin Malami, Dakta Umar Gwandu, shugaba Buhari ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bashi wajen zartar da dokar.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta kawo karshen dokar kulle, ta sanar da lokacin bude Masallatai

Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan dokar ne bayan wata takwas da amincewar tsohuwar majalisar dattijai a kan bawa bangaren shari'a da majalisun jihohi 'yancin cin gashin kansu a harkokin kudi.

Bayan ya amince da dokar, shugaba Buhari ya umarci babban akawu na kasa ya tabbatar da fara aiki da ita.

An kafa kwamitin da zai tabbatar da fara aiki da sabuwar dokar kamar yadda ta ke a karkashin sashe na 121(3) na kundin tsarin mulki da aka yi wa garambawul.

Sai dai, gwamnonin jihohin Najeriya sun nuna adawarsu da rashin amincewarsu a kan zartar da dokar da Buhari ya yi, lamarin da ya sa su ke yanke shawarar tuntubar ministan shari'a domin ganin yadda za a janye dokar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel