Jihohi 36 da aka samu bullar cutar korona a Najeriya - NCDC

Jihohi 36 da aka samu bullar cutar korona a Najeriya - NCDC

- A yanzu cutar korona ta bulla a jihohi 35 na Najeriya da kuma babban birnin kasar na Tarayya

- Jihar Legas ce ke jan ragama inda ta harbi mutum 4,012, 745 suka warke kuma 47 suka kwanta dama

- Jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba cikin dukkanin jihohin Najeriya

- A halin yanzu cutar ta harbi mutum 8,733, sai kuma mutum 2,501 da suka samu waraka, yayin da mutum 254 suka riga mu gidan gaskiya

Watanni uku bayan bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 35 na kasar da babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Kogi ita ce jihar da aka samu bullar cutar karo na farko, inda ta shiga sahun jihohin da cutar ta harba yayin da aka samu mutum biyu dauke da kwayoyin cutar.

Alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Laraba
Alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Laraba
Asali: UGC

Alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Laraba
Alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Laraba
Asali: UGC

Har ila yau dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, sai da masu ruwa da tsaki sun ce rashin kayan aiki da karancin ma'aikatan lafiya ya yi tasiri a kan lamarin.

A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 4,012, sai kuma mutum 745 da suka warke, bayan mutum 47 da suka kwanta dama.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Akwai karancin kayan gwaji da ma'aikatan lafiya a Cross River - PTF

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 8,733, sai kuma mutum 2,501 da suka samu waraka, yayin da mutum 254 suka riga mu gidan gaskiya.

Mun ji cewa kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin yaki da cutar korona a Najeriya PTF, ya zabi wasu magungunan gargajiya uku da ake ikirarin su na maganin cutar korona domin tabbatar da ingancinsu.

Jagoran kwamitin kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya bada shaidar hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba cikin birnin Abuja.

Mustapha ya ce hukumomin da ke da alhakin tantance tasirin magunguna a kasar za su gudanar da bincike akan magungunan uku domin tabbatar da ingancin su ko kuma sabanin haka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel