Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)

Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)

A ci gaba da yakar ta'addanci a yankin arewa maso gabas na kasar nan, dakarun Operation Lafiya Dole na ci gaba da samun nasarori masu tarin yawa ta hanyar halaka mayakan Boko Haram da ISWAP.

Sun yi nasarar halaka wasu mayakan ta'addancin, kwato makamai da kuma ceto wasu wadanda aka yi garkuwa da su.

Sakamakon bayanan sirri da rundunar sojin ta samu a kan maboyar mayakan ta'addancin Boko Haram da ISWAP, rundunar da ke sansani na biyu a Gamboru ta samu nasarar.

Karkashin jagorancin kwamandan bataliya ta uku, dakarun sun fita sintiri inda suka kakkabo sansanin 'yan ta'addan da ke yankin Rann.

A yayin samamen da sojin suka kai, an yi musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da dakarun inda aka halaka 'yan ta'adda biyar tare da samo babura biyu, kekuna 2, amsa-kuwaa 1, batir 1, keken dinki 2 da kuma tutocin Boko Haram 4.

Hakazalika, dakarun sun kara gaba inda suka gano wani kauye mai suna Mudu inda mayakan suka kwace. A nan 'yan ta'addan suka ceto mutum 241 da aka yi garkuwa dasu - mata 105 da kananan yara 136.

Hazikan dakarun sojin sun yi nasarar tarwatsa kauyen tare da sansanin 'yan ta'addan.

Amma kuma, yunkurin damke 'yan ta'addan da ke kauyen Mudu ya tashi a rashin nasara. An yi nasarar kashe mayaka 12 amma sauran sun tsere.

Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)
Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna). Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Hakazalika, a ranar 24 ga watan Mayun 2020, rundunar bataliya ta 151 ta yi nasarar tare mayakan ta'addanci da suka fito da dare don tsallaka wa zuwa Firgi.

Wannan karon da aka yi ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan ta'adda 3 tare da barin wasu da raunika wanda hakan yasa suka tsere tare da barin babura biyu.

Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)
Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna). Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yadda muka yi da mahaifina da na nemi sarautar gargajiya - Ashraf Sanusi Lamido

Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)
Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna). Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A wata nasara ta daban, dakarun sojin sun kai samame a ranar 27 ga watan Mayun 2020 zuwa dajin Sambisa don halaka mayakan ta'addancin da suka tsere.

Kokarin dakarun ya kai ga halakar 'yan ta'adda biyu tare da samo manyan makamai, harsasai, bindigogi da sauransu.

Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna)
Sojin Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 20, sun kwato mutum 241(Hotuna) Hoto daga HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Faruk Yahaya ya jinjinawa dakarun a kan nasarorin da suka samu. Ya yi kira ga dakarun da su dage wajen tabbatar nasarar kawar da ta'addanci a Najeriya.

Janar Faruk ya mika jinjinar shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai ga rundunar a kan wannan aiki tukuru da suka gudanar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
NDA
Online view pixel