Babu korona a jiharmu — Kogi ta yi watsi da sakamakon NCDC

Babu korona a jiharmu — Kogi ta yi watsi da sakamakon NCDC

Gwamnatin jihar Kogi ta ce babu wani mahaluki da ya kamu da cutar COVID-19 da aka fi sani da korona a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa da kwamishinan Lafiya na jihar, Saka Haruna Audu, ya fitar a ranar Laraba ya ce jihar tana da kayan gwaji kuma ta yi gwaje-gwaje masu dimbin yawa kuma duk sun nuna babu mai cutar.

Wannan matsayar ta ci karo da ta Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya, NCDC. Hukumar ta ce mutane biyu sun kamu da COVID-19 a jihar.

Babu korona a jiharmu — Kogi ta yi watsi da sakamakon NCDC
Yahaya Bello. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ranar Yara ta Najeriya: An ta fitar da ƙayatattun hotunan Buhari yana wasa da yara

A cikin sanarwar, Audu ya ce jihar ba za ta amince da wani “labarin kanzon kurege na bullar COVID-19 a jihar ba ”.

Ya ce, "A halin yanzu babu COVID-19 a jihar Kogi. Muna da kayayyakin gwaji isassu kuma munyi darurruwan gwaje gwaje kuma sakamakon ya nuna babu mai cutar."

"Kamar yadda muka fadi a baya, ba za mu amince da wata karya na ikirarin bullar COVID-19 ba shi yasa ba zamu amince da duk wata gwaji da wani dan Kogi ya yi a wani wuri da ba jihar mu ba kuma ba a tuntube mu ba.

"Ba za mu amince da duk wani yunkurin tilasta mana bullar COVID-19 a jihar mu ba."

"A shirye muke mu kula da lafiyar mutanen jihar mu kuma ba mu da shaawar yin siyasa da batun lafiyarsu," in ji shi.

An samu rashin jituwa tsakanin jamian NCDC da suka kai ziyara a jihar Kogi a karo na farko yayin da Gwamna Yahaya Bello ya bayar da umurnin a killacesu na kwanaki 14.

Cibiyar gwajin Korona na jihar Kogi gwaji kwara daya tak ta yi amma ta yi ikirarin tayi gwaji guda 111 da suka nuna babu mai cutar.

Ministan Lafiya Osagie Ehanire ya ce ziyarar da jamian NCDC za su kai a karo na biyu a jihar za ta yi nasara.

Idan baa manta ba alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a daren ranar Laraba ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da korona ya kai 8733 kuma a cikinsu 2 daga jihar Kogi ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel