Korona ta hallaka mutane uku a Kano

Korona ta hallaka mutane uku a Kano

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa annobar korona ta kashe karin mutane uku, lamarin da ya kawo jimillar adadin mutanen da su ka mutu zuwa 41.

A cikin takaitaccen sako da ma'aikatar lafiya ta wallafa a shafinta na tuwita, ta bayyana cewa an sallami jimillar mutane 135, yayin da adadin ma su dauke da cutar ya tsaya a 936 a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Sai dai, ma'aikatar ba ta bayar da cikakken bayani a kan mutum daya da aka sallama da mutane uku da annobar ta kashe ba a ranar Laraba.

Cibiyar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 389 da aka tabbatar sun kamu da cutar korona a ranar Laraba.

Akwai mutane 13 a jihar Kano daga cikin adadin mutanen.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta, an ga cibiyar killace ma su cutar korona ta Kano babu kowa a cikinta, lamarin da ya sa wasu ke zargin cewa ana wasa da hankalin mutane tare da siyasantar da batun cutar.

Korona ta hallaka mutane uku a Kano
Gwamnan Kano a cibiyar killacewa
Asali: UGC

Sai dai, gwamnatin Kano ta zargi ma su yada faifan bidiyon da son kawo rudani tare da jazawa mahukunta bakin jini.

A cewar gwamnatin, ana gyara ne a cibiyar da aka nadi a faifan bidiyon.

Kazalika, gwamnatin ta ce ba a cibiyar ta ke killace ma su cutar korona ba a halin yanzu.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta kawo karshen dokar kulle, ta sanar da lokacin bude Masallatai

Gwamnatin Kano ta sanar da cewa an samu almajirai 28, da ke yawon bara, dauke da kwayar cutar korona, kamar yadda kwamitin yaki da cutar korona a jihar ya sanar ranar Laraba.

Shugaban kwamitin kwashe almajirai daga Kano, Murtala Garo, ya ce, ya zuwa ranar Laraba, gwamnatin Kano ta gwada jimillar almajirai 1,146.

Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi a kan annobar cutar korona a gidan gwamnatin jihar Kano.

"Daga cikin jimillar almajirai 1,146 da mu ka yi wa gwajin cutar korona, an samu 28 da ke dauke da kwayar cutar, yayin da aka gano cewa 311 na dauke da cututtuka daban - daban da su ka hada da zazzabi, gyambon ciki da sauransu," a cewarsa.

Ya kara da cewa gwamnati ta kama wasu almajirai 1,000 da ke gararamba a titunan Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng