Mutane 5 sun mutu, 5 sun jikkata a wani hadari da ya faru a jahar Kano

Mutane 5 sun mutu, 5 sun jikkata a wani hadari da ya faru a jahar Kano

Zuwa yanzu akalla mutane biyar ne suka rasa ransu, yayin da wasu 5 suka samu munanan rauni a wani hadari mai muni da ya faru a jahar Kano a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito hadarin ya auku ne tsakanin motar daukan kaya da karamar mota kirar Golf a Rimin Gata, cikin karamar hukumar Ungogo.

KU KARANTA: Mai babban daki ta karbi bakoncin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Kakaakin hukumar kashe gobara ta jahar Kano,Muhammad Saidu ya bayyana hadarin ya faru ne da misalin karfe 7.18 na safe, inda motocin biyu suka yi taho mu gama da junansu.

Mutane 5 sun mutu, 5 sun jikkata a wani hadari da ya faru a jahar Kano
Wani mummunan hadari
Asali: Facebook

“Motar Tipper Farkas mai lamba QF 435-NSH da wata motar Golf mai lamba KMC-828 ZV sun yi taho mu gama da juna sakamakon gudun wuce sa’a da direbobin motocin suke yi.

“Wani mutumi mai suna Malam Usman Aminu Iguda mazaunin Rimin Gata karamar hukumar Ungogo ne ya shaida mana aukuwar hadarin da misalin karfe 7.18 na safe, samun labarin ke da wuya muka aika jami’anmu don kai agaji.

“Isar mu ke da wuya muka kwashe duka wadanda hatsarin ya rutsa da su zuwa asibitin Murtala, inda a can likitoci suka tabbatar da mutuwar mutane biyar daga cikinsu, yayin da mutane biyar kuma suke samun kulawa.” Inji shi.

A wani labari kuma, Jami’an hukumar tsaron DSS, ta sanar da kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi, mai shekaru 3 a duniya.

Punch ta ruwaito baya ga kama mutumin, jami’an na DSS sun kubutar da yaron cikin ruwan sanyi tare da kwato kudaden fansan da iyayensa suka biya don a sake shi.

A ranar 22 ga watan Mayu ne aka yi garkuwa da jikan Shehi a gidan Shehin dake jahar Kano. Shugaban hukumar DSS reshen jahar Kano, Muhammad Alhassan ya tabbatar da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel