Coronavirus: Akwai karancin kayan gwaji da ma'aikatan lafiya a Cross River - PTF
Kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin yaki da cutar korona a Najeriya PTF, ya fayyace dalilin da ya sa Cross River ta kasance jihar da har yanzu ba a samu bullar cutar korona ba.
Jihar Cross River ta na da karancin kayan gwaji gano masu cutar korona da kuma karancin ma'aikatan lafiya da za su jibinci lamarin cutar kamar yadda kwamitin ya bayyana.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, kwamitin ya tabbatar da wannan ne yayin da ya ziyarci jihar a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu.
Kwamitin ya hadar da jami'ai daga Ma'aikatar Lafiyar ta Tarayya da kuma Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya (NCDC).
Ya kuma lura cewa jihar ta na fama da wasu matsaloli na rashin lura, karancin kayan aiki da kuma karancin matakai da dabaru wajen gano masu cutar.
Sai dai babu shakka kwamitin ya ba da tabbaci dangane da tattaunawar da ya ke da masu ruwa da tsaki domin shawo kan wannan matsaloli.
A Yammacin Larabar da ta gabata ne alkaluman NCDC suka nuna cewa, an samu karin sabbin mutum 389 da cutar korona ta harba a duk fadin Najeriya.

Asali: Facebook
Haka zalika a ranar ne kuma aka samu bullar cutar karo na farko a jihar Kogi, inda aka samu mutum biyu dauke da kwayoyin cutar.
Gabanin ranar Laraba, Kogi da Cross River su ne kadai jihohin da ba a samu bullar cutar ba a duk fadin Najeriya tun bayan bullarta watanni uku da suka gabata.
KARANTA KUMA: Kungiyar Kwadago ta ba wa Ganduje kwanaki 14 ya dawo wa da ma'aikatan Kano albashinsu da ya zaftare
A yayin ganawa da 'yan kwamitin yaki da cutar korona na kasa cikin birnin Abuja, karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora ya ce jihohi da yawa basu shirya wa cutar ba don basu da yawan gadajen jinya da suka kamata.
Ministan yace, "Duk da cewa ba abun mamaki bane, mun yi matukar damuwa da yadda masu cutar ke kara yawa a kasar."
"Akwai yuwuwar yawan masu cutar su wuce yadda ake tsammani tare da wuce yadda Najeriya za ta iya kula da su."
A halin yanzu, alkaluman NCDC sun tabbatar da cewa, cutar korona ta harbi fiye da mutum dubu takwas a jihohi 35 da ta bulla da kuma babban birnin kasar wato Abuja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng