COVID-19: An bukaci gwamnoni su dena tsangwamar almajirai

COVID-19: An bukaci gwamnoni su dena tsangwamar almajirai

Kungiyar musulunci ta Jam’iyyatu Ansariddeen Attijjaniyya (JAA) ta bukaci gwamnonin da suke mayar da almajirai su dena abin ta da kira “tsangwamar almajiran.”

A sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren ta, Sayyidi Muhammad AlQasim Yahaya, JAA, ta ce tun farko gwamnonin suka gaza kulawa da almajirai tsawon shekaru da suka wuce don haka ba su da damar cin zarafinsu da sunan yaki da COVID-19.

Kungiyar ta ce tana goyon bayan kokarin da gwamnatoci ke yi wurin yaki da annobar amma ba ta goyi bayan yadda ake tilastawa almajirai barin garuruwan da suke zaune ba.

COVID-19: An bukaci gwamnoni su dena tsangwamar almajirai
Almajirai. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ranar Yara ta Najeriya: An ta fitar da ƙayatattun hotunan Buhari yana wasa da yara

Wani sashi na sanarwar ta suka fitar ta ce, "JJA tana kira a dena tsangwaman almajirai a kasar nan take kuma a rika mutunta hakkinsu na yan kasa da suke da shi na zama a duk inda suke so.

"Muna kuma kira ga gwamnoni su dauki matakan da suka dace na gwamutsa almajiranci cikin tsarin ilimin zamani kuma su biya diyya ga malamai da daliban makarantun allo saboda cin zarafinsu."

Kungiyar musuluncin ta kuma yi kira ga hukumomi su bude masallatai domin mutane su samu daman cigaba da ibada tare da kira ga masallata su bi dokokin kiyaye yaduwar cutar.

JJA ta cigaba da cewa akwai bukatar ayi bitar tsarin da hukumomin tsaro ke amfani da shi wurin taki da garkuwa da mutane da 'yan bindiga musamman a jihohin arewa.

A wani labarin, kunji cewa daraktan kungiyar rajin kare hakkin Musulmi (MURIC), Ishaq Akintola ya ce gwamnoni da suka bari aka yi sallar Idi a jam'i sun yi babban laifiin da ya kamata a tsige su daga kujerunsu.

A ranar Lahadi, an yi sallar Idi a Jam'i a jihohi masu tarin yawa na fadin kasar nan. Wannan kuwa take doka ce tare da rashin biyayya ga umarnin kwamitin yaki da cutar korona na kasa baki daya.

An yi sallolin ne a cunkushe ba tare da saka takunkumin fuska ba duk da cincirindon jama'a.

A misali, jihar Kano wacce a halin yanzu take a ta biyu a yawan masu cutar korona a kasar nan, ta yi sallar idi da cincirindon mutane.

A wata takarda da kungiyar ta fitar, Akintola ya ce abin da gwamnoni suka yi ya sha bambam da umarni gwamnatin tarayya, Jama'atu Nasril Islam da kuma majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci ta Najeriya.

Ya bukaci 'yan majalisar jihohin da abun ya shafa da su yi abinda ya dace akan abinda gwamnonin suka yi don laifin ya cancanci tsigewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel