Sokoto: 'Yan bindiga sun halaka mutum 60 a harin da suka kai wasu kauyuka
Kamar yadda rahotanni daga jihar Sokoto suka bayyana, an kashe mutum kusan 60 a cikin wasu hare-haren da 'yan bindiga suka kai a ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2020 a wasu kauyuka na karamar hukumar Sabon-Birnin-Gobir.
Ganau ba jiyau ba, sun ce maharan sun dauki tsawon sa'o'i suna ruwan wuta a kauyukan ba tare da kowa ya tunkaresu ba.
Hakazalika, wata mata da 'yan bindiga uku sun mutu a cikin wani harin da suka kai karamar hukumar Gwadabawa ta jihar.
Wani jami'in da ya samu zuwa inda al'amarin ya faru, ya sanar da BBC cewa, da misalin karfe uku zuwa biyar na yammacin Laraba ne suka samu labarin cewa mutane sun taso da babura kusan 100 daga daji.
Mutanen sun taho ne daga dajin da ke kusa da Issa sannan sun nufi kauyukan.
A cewarsa, "Koda muka samu labari, mun je mun sanar da jami'an tsaro abinda ke faruwa. Daga nan sai mutanen suka isa garin Garki zuwa garin Dan Adu'a."
Jami'in ya kara da cewa, "A garin Dan adu'a ne muka samu gawawwaki 13 kwance banda wadanda aka nema aka rasa a garin.
"A garin Garki kuwa abin da idanuna suka nuna mini har na dauki hoto, na ga gawawwaki 19 cif."
Ya kara da cewa, "A garin Kuzari, an kashe mutum 20 har da limamin garin A garin Kafi kuwa an kashe mutum 6, garin Masawa an harbi mutum 2."
Ya tabbatar da cewa jimillar gawawwakin da ya gani sun kai ta mutum 60 banda wadanda ake nema ba a gansu ba.
KU KARANTA: Boko Haram: Yadda Dapchi ta koma 'kufai' bayan harin 'yan ta'adda (Hotuna)
Ya ce, "Barayin shanu da mutane ne suka kai wadannan harin. Mai girma gwamnan jihar kuwa ya kai jaje Sabon Birni a makon da ya wuce domin jajanta wa mutanen garin bisa ga kashe mutum 19 da aka yi."
Ya kara da cewa, "Batun jami'an tsaro kuwa, mun shaida musu abinda ke faruwa kuma sun je garin Garki amma basu da kayan aikin da za su fafata da wadannan 'yan bindigar.
"Baya ga rashin isassun kayan aiki, su kansu jami'an tsaron ba su da yawan da za su tunkari 'yan bindiga 100 da suka kawo harin."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng