Yadda muka yi da mahaifina da na nemi sarautar gargajiya - Ashraf Sanusi Lamido

Yadda muka yi da mahaifina da na nemi sarautar gargajiya - Ashraf Sanusi Lamido

Dan tsohon sarkin Kano, Ashraf Sanusi Lamido, ya bayyana cewa a wani lokaci ya bukaci mahaifinsa da ya bashi mukamin sarautar gargajiya a zamanin da yake sarkin Kano.

A hirar da Ashraf yayi da BBC kai tsaye a shafinsa na Instagram, ya ce da ya bukaci hakan sai mahaifinsa yace masa ya je ya ci gaba da karatu zuwa wani lokaci a gaba sannan a duba bukatarsa.

"Na aike wa Takawa (Sarki Muhammadu Sanusi II) sako ta WhatsApp cewa yaushe za a bani sarautar gargajiya, amma sai yace in ci gaba da karatu," cewar Ashraf.

Ya kara da cewa, lokacin da aka nada mahaifinsa a matsayin Sarkin Kano, an gargadi kannansa da su daina turanci a cikin gida sai harshen Hausa.

Da aka tambayi dan tsohon basaraken ko yana da wani buri na mulkin siyasa, sai ya bayyana cewa ya fi son jama'a su duba cancantarsa a kan wani abu sannan sai ya duba yuwuwar neman mulkin.

Ya sake cewa, "Idan har shiga siyasa za ta sa in kauce wa addini, toh ba zan shiga ba."

Ashraf ya bai wa matasa shawarar mayar da hankali wajen neman ilimi domin kada su fada cikin duhu.

Yadda muka yi da mahaifina da na nemi sarautar gargajiya - Ashraf Sanusi Lamido
Yadda muka yi da mahaifina da na nemi sarautar gargajiya - Ashraf Sanusi Lamido. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Ya kara kira ga matasa da su yi taka-tsan-tsan da yadda suke amfani da shafukan sada zumunta. Su dinga amfani da su ta hanyar da ya kamata.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Jihar Kaduna ta sake tsawaita dokar hana zirga-zirga (Bidiyo)

A wani labari na daban, Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta kama maza hudu dauke da kawunan mutum biyar. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Tee Leo Ikoro, ya sanar da jaridar Daily Trust cewa ana ci gaba da bincikar lamarin tare da bankado masu hannu a ciki.

Wadanda ake zargin duk masu hakar kabari ne, kuma sun shiga hannu ne a ranar Litinin bayan fito da wata gawa da aka birne bayan kwanaki biyu da suka yi.

An gano sunan mutanen da Oluwadare Idowu mai shekaru 67, Adewale Abiodun mai shekaru 40, Akinola Sunday mai shekaru 69 da kuma Seun Olomofe mai shekaru 45.

Lamarin ya faru ne a wata makabarta da ke karamar hukumar Akure ta yamma a jihar Ondo inda wadanda ake zargin suke aiki.

Wasu daga cikin 'yan uwan mamacin ne suka je makabartar don yin kankare a kabarin dan uwansu, amma sai suka gane cewa an cire kan gawar dan uwan nasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng