Kungiya ta siya wa gwamnan APC fom din takara

Kungiya ta siya wa gwamnan APC fom din takara

- Wata kungiyar masu goyon bayan Gwamna Obaseki na jihar Edo ta saya masa fom din takarar zaben fidda gwani a karkashin jam'iyyar APC

- Kungiyar ta ce mutane masu raayin ganin Gwamna Obaseki ya zarce ne na gida da kasashen waje suka tara masu kudi Naira miliyan 22.5 don sayan fom din

- Kungiyar ta ce ta gamsu da irin kamun ludayin Gwamna Obaseki kuma tana ganin ya fi dukkan sauran masu neman takarar tikitin cancanta

Wata kungiya ta magoya bayan gwamnan Edo, Godwin Obaseki mai suna 'The Obaseki Mandate Forum' ta siya masa fom din takarar zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC).

A yayin taron manema labarai da ta kira a ranar Laraba, Nathaniel Momoh, shugaban kungiyar ya ce kungiyar ta gamsu da irin kamun ludayin gwamnan ne kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kungiya ta siya wa gwamnan APC fom din takara
Kungiya ta siya wa gwamnan APC fom din takara. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

Jam'iyyar mai mulki a jihar ta tsayar da ranar 22 ga watan Yuni domin zaben dan takararta da zai wakilce ta a zaben gwamna da za a yi a ranar 19 ga watan Satumban 2020.

KU KARANTA: A tsige gwamnonin da suka bari aka yi sallar Idi a jihohinsu, in ji MURIC

Momoh ya ce mutanen jihar Edo na gida da wadanda suke kasashen waje ne suka tara kudaden da aka saya fom din.

Ya ce, "Abokan mu yan jarida, za ku yi mamakin sanin cewa mutane masu raayi ganin cigaban mulki na gari ne suka tara kudi Naira miliyan 22.5 don sayan fom din."

"Suna son ganin gwamnan ya cigaba da inganta walwalar mutane da gine gine da Gwamnan mu Godwin Obaseki ya fara tun hawarsa kujerar mulki.

"Mun yi imanin cewa wanda mutane ke so ne zai samu tikitin wakiltar jam'iyyar mu lokacin da za a gudanar da zaben fidda gwani a ranar 22 ga watan Yuni.

"Mun gamsu cewa babu wani dan takara cikin wadanda aka ambaci sunansu kawo yanzu da ya fi Gwamna Godwin Obaseki dacewa da wakiltar jamiyyar.

"Munyi imanin cancantarsa za ta saka ya yi nasara kuma ya wakilci jam'iyyar a zaben gwamnan inda nan ma zai sake nasara don cigaba da ayyukan alheri a jihar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel