Korona: Najeriya ta samu karin mutum 389, yanzu mutum 8733 suka kamu

Korona: Najeriya ta samu karin mutum 389, yanzu mutum 8733 suka kamu

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 389 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.45 na daren ranar Laraba, 27 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 389 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-256

Katsina-23

Edo-22

Rivers-14

Kano-13

Adamawa-11

Akwa Ibom-11

Kaduna-7

Kwara-6

Nasarawa-6

Gombe-2

DUBA WANNAN: Sallar Idi: 'Yan sanda sun kama manyan malamai 3 a Zaria

Plateau-2

Abia-2

Delta-2

Benue-2

Niger-2

Kogi-2

Oyo-2

Imo-1

Borno-1

Ogun-1

Anambra-1

Kamar yadda alkaluman suka nuna, a karo na farko an samu bullar kwayar cutar ta korona a jihar Kogi bayan an ta dauki ba dadi tsakanin gwamnan jihar, Yahaya Bello da hukumar ta NCDC.

Da farko dai Gwamna Bello ya nuna cewa babu bukatar ayi gwaji a jiharsa duba da saboda babu wanda ya nuna alamun cutar.

Daga bisani ya kuma ce jiharsa tana da wata manhaja na musamman da ke iya gano mai cutar kamar yadda ya fadi a wani hira da aka yi da shi a gidan talabijin.

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Laraba 27 ga watan Mayun 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 8733.

An sallami mutum 2501 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 254.

A wani labarin kun ji cewa wata kungiya ta magoya bayan gwamnan Edo, Godwin Obaseki ta siya masa fom din takarar zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jamiyyar ta All Progressives Congress (APC).

A yayin taron manema labarai da ta kira a ranar Laraba, Nathaniel Momoh, shugaban kungiyar ya ce kungiyar ta gamsu da irin kamun ludayin gwamnan ne kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Jamiyyar mai mulki a jihar ta tsayar da ranar 22 ga watan Yuni domin zaben dan takararta da zai wakilce ta a zaben gwamna da za a yi a ranar 19 ga watan Satumban 2020.

Momoh ya ce mutanen jihar Edo na gida da wadanda suke kasashen waje ne suka tara kudaden da aka saya fom din.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel