Mai babban daki ta karbi bakoncin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Mai babban daki ta karbi bakoncin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ma mahaifiyarsa, Mai babban daki ziyara a gidanta dake unguwar Gwangwazo, dan tazara kadan daga fadar masarautar Kano.

Daily Trust ta ruwaito Sarki ya kai ziyarar ne tare da rakiyar fadawansa kalilan, inda suka bar fada da misalin karfe 10 na safiya a cikin motarsa kirar Rolls Royce, kuma ta Kofar Kudu ya bi.

KU KARANTA: Jami’an DSS sun kama mutumin da ya yi garkuwa da dan gidan Dahiru Bauchi

Mai martaba Sarki ya kwashe tsawon mintuna 45 a gidan mahaifiyar tasa, daga nan kuma ya tashi ya koma fada domin shirin wata ziyara da zai kai zuwa gidan Nassarawa.

A gidan Nassarawa, Sarki Bayero ya yi ma tsofaffin Sarakuna da aka binnesu a gidan addu’o’I, kamar dai yadda kowanne Sarki yake yi a yayin hawan Nassarawa.

Mai babban daki ta karbi bakoncin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Sarkin ya jinkirta ziyarar Mai Babban Daki ne zuwa rana ta 4 bayan Sallah ba kamar yadda aka saba yi a ranar Hawan Daushe ba, saboda dokar gwamnati ta dakatar da hawan Sallah.

Gwamnati ta soke hawan ne don dakile yaduwar cutar Coronavirus, don haka ko a lokacin da Sarkin zai tafi gidan Nassarawa, da fadawa yan kadan ya tafi.

Gwamnati ta dakatar da hawan Sallah a dukkanin masarautun jahar guda biyar, duk da cewa ta bada umarnin gudanar da sallar Idi da sallar Juma’a, wanda a baya ta hana saboda cutar.

Da ba don wannan annobar ba, kamata ya yi wannan sallar ta zamto hawar mai martaba Sarkin ta farko tun bayan darewarsa mukamin sarauta bayan Ganduje ya sauke Sarki Sunusi.

Aminu ya kasance Sarkin Bichi mai daraja ta daya bayan Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu hudu, a 2019, a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020 kuma ya nada shi sabon Sarkin Kano.

A wani labari, Jami’an hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta sanar da kama mutumin da ya yi garkuwa da jikan fitaccen Malamin addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi, mai shekaru 3 a duniya.

Punch ta ruwaito baya ga kama mutumin, jami’an na DSS sun kubutar da yaron cikin ruwan sanyi tare da kwato kudaden fansan da iyayensa suka biya don a sake shi.

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu aka yi garkuwa da shi a gidan Shehin dake jahar Kano. Shugaban hukumar DSS reshen jahar Kano, Muhammad Alhassan ya tabbatar da lamarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel