Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Sa'in Bichi, Hakimin Dambatta, Dr. Wada Ibrahim Waziri, rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Sa'in Bichi, Hakimin Dambatta, Dr. Wada Ibrahim Waziri, rasuwa

Inna liLLAhi wa inna IlaHI Raji'un! Allah ya yiwa Dr. Wada Ibrahim Waziri, Sa'in Bichi kuma Hakimin Dambatta, rasuwa ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2020. The Nation ta ruwaito.

Rahoton ya bayyana cewa dattijon ya rasu ne bayan gajeruwar jinya yana mai shekara 89 a duniya.

Marigayi Hakimin Dambatta dan gidan sarauta ne kuma yayi karatunsa na fari a makarantar birnin Kano gabanin samun yancin kan Najeriya.

Yanzu-yanzu: Allah ya yiwa Sa'in Bichi, Hakimin Dambatta, Dr. Wada Ibrahim Waziri, rasuwa
Dr. Wada Ibrahim Waziri
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng