Dokar cin-gashin-kan majalisar jihohi da bangaren shari’a: Gwamnonin Najeriya za su gana ranar Laraba

Dokar cin-gashin-kan majalisar jihohi da bangaren shari’a: Gwamnonin Najeriya za su gana ranar Laraba

A yau Laraba, gwamnonin jihohin Najeriya za su gana domin tattauna batutuwa a kan dokar ba wa majalisun jihohi da bangaren shari'a 'yancin kai a fannin sha'anin kudi.

Cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar gwamnonin Najeriya NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya fitar a ranar Talata cikin birnin Abuja, ta nuna cewa a yau Laraba gwamnonin kasar za su gana da juna.

Wannan shi ne zama na tara cikin jerin ganawa ta nesa-nesa da gwamnonin Najeriya su ka yi ta hanyar bidiyo tun bayan bullar cutar korona a kasar.

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2020, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan wannan doka da ta ba majalisar dokoki da hukumomi shari'a na jihohi damar cin gashin kansu.

Sabuwar dokar mai suna 'The Executive Order 10, 2020' da shugaba Buhari ya rattaba hannu a kai, za ta ba wa majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi damar samun kudadensu kai-tsaye ba tare da ya bi ta hannun gwamnoni ba.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF)
Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF)
Asali: Facebook

A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya ba wa Ofishin Akanta Janar na kasa umarnin cire wa majalisar dokoki da bangaren shari’a kudaden su daga asusun duk wata jiha da ta ki bin wannan umarni.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnonin jihohi da dama sun girgiza da wannan mataki da shugaban kasar ya dauka.

KARANTA KUMA: An cafke 'yan fashi 2 masu kwacen keke napep a Anambra

Sai dai domin gano ina suka dosa, Bello-Barkindo ya ce, ganawar gwamonin za ta fara ne da misalin karfe 2.00 na ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, kuma dukkanin gwamnonin jihohi 36 na kasar za su halarta su na zaune a jihohinsu ta hanyar bidiyo.

Sauran batutuwar da gwamnonin za su tattauna a kai kamar yadda Barkindo ya bayyana sun hadar da tababar da ta mamaye kudirin Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC).

Sai kuma batutuwan da suka shafi mallakar kamfanin sarrafa iskar gas na kasa (NLNG) da kuma halin da ake ciki game da annobar korona a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel