Abba Kyari: Buhari bai taba mika ikon ofishinsa ga kowa ba - Fadar Shugaban kasa

Abba Kyari: Buhari bai taba mika ikon ofishinsa ga kowa ba - Fadar Shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan wasu rahotanni da ke yawo a kafafen yada labarai a kan cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya warware nadin wasu mukamai da tsohon shugaban ma'aikatansa, Abba Kyari, ya sanar.

A cikin jerin wasu sakonni da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya wallafa a shafinsa na tuwita, ya ce ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin rahoton da ake yadawa.

Garba Shehu ya ce rashin gaskiyar rahoton ne ya sa kafafen da ke yada labarin su ka ce wata majiya marar tushe, da aka kasa bayyanata, ta sanar da su.

"Hankalin fadar shugaban kasa ya kai kan wani rahoto da wasu kafafen yada labarai ke yadawa a kan cewa shugaban kasa ya warware wasu nadin mukamai da soke wasu takardu masu dauke da sa hannun tsohon shugaban ma'aikatansa, marigayi Abba Kyari.

"Ba mu yi mamaki ba da masu yada labarin su ka ce wata majiya da ba zasu iya ambaton sunanta ba ta tabbatar mu su da faruwar hakan.

"Babu kamshin gaskiya a cikin rahoton, kuma ya kamata 'yan Najeriya su yi watsi da shi.

"Mutanen Najeriya ne su ka sake zaben shugaba Buhari a watan Fabrairu na shekarar 2019. Bai taba ba, kuma ba zai taba mika ikonsa ga wani ba, 'yan Najeriya ne su ka bashi wannan iko saboda sun yarda da shi," a cewar Garba Shehu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel