Ranar Yara ta Najeriya: An ta fitar da ƙayatattun hotunan Buhari yana wasa da yara
- Fadar shugaban kasa ta fitar da wasu ƙayatattun Shugaba Muhammadu Buhari tare da kananan yara
- Femi Adesina, mashawarcin Shugaba Buhari a fanin kafafen watsa labarai ne ya fitar da hotunan don bikin ranar yara ta Najeriya a ranar 27 ga watan Mayu
- Shima mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya wallafa wasu hotunansa tare da yara don murnar bikin ranar yaran ta 2020
Fadar shugaban kasar Najeriya ta fitar da wasu kyawawan hotunan Shugaba Muhammadu Buhari yana cuɗanya da yara ƙanana.
Kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, mashawarcin shugaban ƙasar a kan kafafen watsa labarai, Femi Adesina ne ya wallafa hotunan don nuna yadda Shugaban kasar ya ke mu'amala da yara a yayin da ake bikin ranar yara ta Najeriya.
Ana bikin ranar yaran ta Najeriya a ranar 27 ga watan Mayun ko wane shekara. Adesina ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook.
Ga wasu daga cikin hotunan a kasa.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: An sako malamin addinin musulunci da aka kama saboda 'zagin' El-Rufa'i

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
A bangarensa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo shima ya wallafa wasu hotunansa don murnar ranar yaran Najeriya ta shekarar 2020.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, Osinbajo ya yi murnar zagayowar ranar ta yaran Najeriya inda ya yi kira da a bawa yara dama domin su aikata abinda ya fi wanda magabatansu suka aikata.
Hakazalika, shima Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya taya yaran Najeriya murnar zagoyowar ranar ta su na shekarar 2020.
Shima ya taya yaran murnar zagayowar ranar da ya ce an ware domin inganta walwala da jin dadinsu na yanzu da kuma gaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng