MURIC ta nemi a tsige gwamnonin da suka bari aka yi sallar Idi a jihohinsu

MURIC ta nemi a tsige gwamnonin da suka bari aka yi sallar Idi a jihohinsu

Daraktan kungiyar rajin kare hakkin Musulmi (MURIC), Ishaq Akintola ya ce gwamnoni da suka bari aka yi sallar Idi a jam'i sun yi babban laifiin da ya kamata a tsige su daga kujerunsu.

A ranar Lahadi, an yi sallar Idi a Jam'i a jihohi masu tarin yawa na fadin kasar nan. Wannan kuwa take doka ce tare da rashin biyayya ga umarnin kwamitin yaki da cutar korona na kasa baki daya.

An yi sallolin ne a cunkushe ba tare da saka takunkumin fuska ba duk da cincirindon jama'a.

A misali, jihar Kano wacce a halin yanzu take a ta biyu a yawan masu cutar korona a kasar nan, ta yi sallar idi da cincirindon mutane.

A wata takarda da kungiyar ta fitar, Akintola ya ce abin da gwamnoni suka yi ya sha bambam da umarni gwamnatin tarayya, Jama'atu Nasril Islam da kuma majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci ta Najeriya.

Ya bukaci 'yan majalisar jihohin da abun ya shafa da su yi abinda ya dace akan abinda gwamnonin suka yi don laifin ya cancanci tsigewa.

"Abin kunya ne yadda gwamnonin suka saki rayukan mutane suna wasa da su. Wannan ba musulunci bane kuma ba addini bane," Akintola yace.

"Dole ne a hukunta mutane masu mulki matukar suka yi wasa da rayukan jama'ar da suke mulka. Wannan abu daya tak ya saka rayukan jama'a cikin hatsari kuma makonni biyu kacal za mu jira kafin bayyanar sakamakon abinda gwamnonin suka yi.

“Ba haka ake bautar Allah ba, kuma ba ta wani shagalin biki ake ba. MURIC kungiya ce ta masu rajin kare hakkin dan Adam kuma ba za ta kare duk wanda bai kyauta ba. Musulunci addini ne mai adalci.

MURIC ta nemi Buhari ya tsige gwamnonin da suka bari aka yi sallar Idi a jihohinsu
Farfesa Ishaq Akintola. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An sako malamin addinin musulunci da aka kama saboda 'zagin' El-Rufa'i

"Don haka ba za mu kaskantar da kanmu ba wajen sauya doka don cimma wata manufa ba ko kuma saboda gwamnonin Musulmai ne.

“Idan an ga muna assasa karfafa hakkokin jama'a, toh daga cikin wadanda Allah ya bayyana ne ba wai na dan Adam ba. Bayan nan, ai Kiristoci sun yi bikin Ista amma babu wani shagali da suka yi. Me zai sa mu ma ba za mu iya hakan ba?

“Idan muna da 'yan majalisa a jihohinmu kuma sun san hakkinmu, dole ne su tashi su kare mu.

“A takaice dai, gwamonin arewa da suka bari aka yi sallar Idi sun yi laifin da ya kamata a tsige su a shari'ance. A don haka muna kira ga 'yan majalisar jihohin da su yi abinda ya dace.

"Gwamnoninmu basu damu da rayukanmu ba. Ko dai su fito su bada hakuri, ko kuma su tattara su sauka daga mulki ko kuma a tsigesu."

Akintola ya mika ban hakurinsa ga 'yan Najeriya a madadin dukkan Musulmin Najeriya.

Ya kara da yin kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi magana a kan al'amarin da ya kwatanta da tozarci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel