Ruwan sama ya lalata kayan abinci da FG ta bawa Kano tallafi

Ruwan sama ya lalata kayan abinci da FG ta bawa Kano tallafi

Rahotanni sun bayyana cewa ruwan sama ya lalata dumbin kayanci da gwamnatin tarayya (FG) ta bawa jihar Kano da niyyar a rabawa talakawa domin rage mu su radadin matsin tattalin arzikin da bullar annobar korona ta haifar.

A ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu, ma'aikatar walwala, jin kai da bayar da tallafi ta bawa gwamnatin jihar Kano tallafin manyan motocin kayan abinci 139.

Kayan abincin da aka bayar domin rabawa talakawa da marasa karfi sun hada da shinkafa, gero, masara, dawa da maiwa.

Daily Nigerian ta rawaito cewa kayan abinci sun kunshi buhun shinkafa mai nauyin 50kg guda 6000, buhun masara guda 42,600, da na dawa guda 17,400.

Sauran sun hada da buhun gero guda 17,400 da kuma jarkokin man girki ma su girman 20ltr guda 2000.

Ruwan sama ya lalata kayan abincin N4bn da FG ta bawa Kano tallafi
Ruwan sama ya lalata kayan abincin da FG ta bawa Kano tallafi
Asali: UGC

Bayan karbar kayan, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin a jibgesu a harabar kamfanin kayan noma na jihar Kano (KASCO) wanda ke daura da yankin 'Farm Center' a birnin Kano.

A cewar gwamnan, ya zabi a ajiyesu a KASCO ne saboda za a fi samun saukin raba kayan ga mabukata daga wurin.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta kawo karshen dokar kulle, ta sanar da lokacin bude Masallatai

Daily Nigerian ta lura cewa kusan wata guda da bayar da tallafin, amma an barsu a harabar kamfanin rana da ruwa na karewa a kansu ba tare da an rabawa jama'a ba.

Jaridar ta ce ruwan sama ya shanye wasu buhunhunan gero, sun nutse a cikin ruwan sama mai yawa da aka lafta a sassan birnin Kano ranar Litinin.

Da ya ke magana a kan faruwar lamarin, shugaban kwamitin neman tallafin kudin taimakon yaki da annobar korona a Kano, Farfesa Yahuza Bello, ya ce an shirya fara rabon kayan ne daga ranar Alhamis mai zuwa.

Wani mamba a kwamitin da ya nemi a boye sunansa ya ce bai yarda cewa ruwan sama ya lalata ma fi yawan bangaren kayan abincin ba.

"Rahoton karya ne. Ku je ku gani, za ku ga an rufe buhunhunan kayan abincin da tamfol mai karfi da gwamnati ta karbo haya," a cewarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel