Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sheikh Laidi Orunsolu rasuwa

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sheikh Laidi Orunsolu rasuwa

Shugaban Kungiyar Limamai da malaman addinin musulunci ta jihar Ogun kuma babban Limamin kasar Egba, Alhaji Liadi Orunsolu ya rasu.

Babban malamin ya rasu ne a safiyar ranar Talata 26 ga watan Mayun shekarar 2020 a gidansa da ke Abeokuta kamar yadda TVC ta ruwaito.

Ya rasu yana da shekaru 99 a duniya.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sheikh Laidi Orunsolu rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Sheikh Laidi Orunsolu rasuwa. Hoto daga TVC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kano: Yadda wani bawan Allah ya yanke jiki ya fadi ya mutu bayan gama sallar Idi

Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun a ranar Talata ya mika sakon ta'aziyarsa bisa rasuwar Sheikh Liadi Ayinde Orunsolu.

Cikin sakon da gwamnan ya rattaba hannu da kansa, ya yi wa al'ummar jihar da musulmi musamman mutanen kasar Egba taaziyar rasuwar limamin.

Gwamnan ya ce rasuwar Orunsolu babban rashi ne ga jihar inda ya bayyana cewa marigayi shugaban limaman ya karasa rayuwarsa ne yana koyar da halaye masu kyau da darussa daga Al Kurani mai girma.

Ya kara da cewa rasuwar babban malamin babban rashi ne a wurinsa.

Ya ce, "Baba Orunsolu ya yi rayuwa mai kyau da darrusa masu yawa da za a rika tunawa da su. Ina kira ga musulmi a jihar su cigaba da raya shi ta hanyar cigaba da aikata ayyukan alheri da ya koyar lokacin rayuwarsa.

"Zan yi kewar karamcinsa. Baya fargabar fadawa masu mulki gaskiya kuma yana daya daga cikin masu goyon bayan gwamnatinmu.

"Alakar mu kamar ta 'da da mahaifi ne bai dauki ne a matsayin gwamna ba. Ba ya boye gaskiya wurin magana a kan harkokin da ya shafi walwalar mutanen jihar mu.

"Tsawon rai da Allah ya bashi na yin watan azumin Ramadan da yin sallar idi a shekarunsa na 99 alama ce da ke nuna Allah ya albarkaci rayuwansa.

"Ina adduar Allah ya gafarta masa ya saka masa da gidan Aljannah Firdaus kuma ya bawa iyalansa hakurin jure rashinsa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel