Korona: Bidiyon yadda wata mata ta ke murna bayan an ba ta gado a cibiyar killacewa
Faifan bidiyon yadda wata mata ta cika da murna bayan an ba ta gado a cibiyar killace ma su cutar korona ya bawa jama'a a mamaki.
A cikin faifan bidiyon, wanda ya yi farin jini a dandalin sada zumunta, matar ta nuna gadonta a cikin dogon da ake killace ta tare da sauran ma su cutar korona.
Duk da ba ta bayyana wurin da cibiyar ta ke ba, matar ta nunawa mabiyanta a dandalin sada zumunta gadon da ta aka ba ta.
Matar ta kasance cikin farin ciki da jin dadi yayin da ta ke nadar faifan bidiyon gadonta tare da bayyana cewa har na'urar sanyaya daki.
"Nan ne cibiyar killacewa, kun gani, har da na'urar sanyaya daki. Wannan ne gadona, shine gadona, gadona ne," kamar yadda matar ke fada cikin farin ciki da jin dadi.
Kalli faifan bidiyon a kasa;
A ranar 19 ga watan Mayu ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa Susan Idoko Okpe, mace ta farko da aka sanar ta kamu da cutar korona a jihar Benuwe, ta sake rokon gwamnatin Najeriya a kan ta saketa daga cibiyar killacewa ta Abuja bayan ta shafe kwanaki 57.
DUBA WANNAN: Muhimman bayanai sun fito a kan silar rikicin Pantami da Dabiri
A wani sabon faifan bidiyo da ta nada ranar Talata, Susan ba ta san me NCDC ke nufi da ita ba tare da yin zargin cewa ana son kasheta ko ba ta guba.
Susan ta kafe a kan cewa lafiyarta kalau kuma tunda aka kaita cibiyar killacewa ba a duba lafiyarta ba.
Ta bayyana cewa sau biyar ana yi mata gwajin kwayar cutar korona amma ba a sanar da ita sakamakon gwajin.
Ta roki hukuma da mahukunta a kan saketa, su kyaleta ta koma gida wurin iyalinta domin cigaba da rayuwa cikin 'yanci.
"An yi min gwaji na farko, na biyu, na uku da na hudu amma su na cewa na ki amincewa a sake yi min gwaji. An sake daukan jinina ranar Alhamis domin yi min gwaji na biyar.
"Ina son 'yan Najeriya su taimakeni, su tambayi NCDC me suke nufi da ni?
"Lafiyata kalau, ban taba yin rashin lafiya ba tunda aka kawoni nan tsawon kwanaki 57 da suka gabata.
"Ba su bani wani magani ba. Ban yi rashin lafiya ba, babu ciwon ko kai, ban yi tari ba, amma har yanzu ina nan a kulle, babu wanda ya ke zuwa ya wurina, na gaji," a cewar Susan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng