An sako malamin addinin musulunci da aka kama saboda 'zagin' El-Rufa'i

An sako malamin addinin musulunci da aka kama saboda 'zagin' El-Rufa'i

Rundunar 'Yan sanda a jihar Kaduna sun sako malamin addinin musulunci mazaunin Sokoto, Bello Yabo, da aka kama kuma aka tafi da shi Kaduna a ranar Juma'a.

An kama Yabo ne saboda cin zargin Gwamna Nasir El Rufa'i na jihar Kaduna da aka ce ya yi saboda hana yin sallar Idi a jihar.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta, Yabo ya yi Allah wadai da El Rufai da wasu malaman addinin musulunci a jihar a kan cigaba da rufe masallatai da hana taron addini.

A bidiyon, malamin ya yi tir da gwamnan na jihar Kaduna da Kwamitin malaman addinin musulunci na jihar saboda abinda ya kira kyalle ‘karamin tsuntsu’ ya fada musu abinda za suyi.

An sako malamin addinin musulunci da aka kama saboda 'zagin' El-Rufa'i
An sako malamin addinin musulunci da aka kama saboda 'zagin' El-Rufa'i. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kora daga ofis: Pantami da Dabiri-Erewa sunyi musayar zafafan kalamai

Daily Trust ta ruwaito cewa yan sanda a ranar Asabar sun tabbatar mata da kama malamin da aka dakko shi daga Sokoto zuwa Kaduna don ya bayar da bayani a kan zargin da gwamnatin jihar Kaduna ke masa.

Sai dai a yammacin ranar Litinin, majiyar Legit.ng ta gano cewa an bayar da belin Yabo bayan wani fitaccen lauya a jihar Kaduna ya tsaya masa.

An gano cewa ya ce ba zai fada wa yan sanda komi ba idan ba su fada masa inda aka samo bidiyon ba tunda a cewarsa wannan ba shine karo na farko da ake amfani da fasahar zamani a dauki murya mai kama da na sa.

Da aka tuntubi Kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jaligi a kan lamarin, ya ce abinda zai iya tabbatarwa kawai shine an bayar da belin malamin a daren ranar Lahadi.

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani bawan Allah da ba a bayyana sunansa ba ya yanke jiki ya mutu a yayin da ake bikin sallar Idi a unguwar Sharada a jihar Kano.

Vangaurd ta ruwaito cewa mutumin ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu ba da dadewa ba bayan ya gama sallar raka'a biyu na Idi a Kano.

Wata majiya da ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ba ta fadi sunan mutumin ba ta ce mutumin ya fito daga unguwar Kofar Dan Agundi ne domin ya yi sallar Idi a Sharada.

Acewarsa, "Ba mu san sunanshi ba, ko adireshinsa ko inda ya ke aiki da sauran bayanai.

"Mun dai san daga Kofar Dan Agundi ya taho domin yin salla a Sharada. Ya yanke jiki ya fadi bayan an kammala sallar."

"Yan uwansa da jamian hukumar Hisbah sun dauke gawarsa. Sun koma da shi Kofar Dan Agundi inda aka yi masa jana'iza bisa tsarin koyarwar addinin musulunci," a cewar majiyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel