COVID-19: Mace-mace na tada hankulan mazauna birnin Katsina da Daura

COVID-19: Mace-mace na tada hankulan mazauna birnin Katsina da Daura

Tsoro da tashin hankali ya shiga zukatan mazauna jihar Katsina sakamakon karuwar mace-mace a garin Katsina bayan hauhawar annobar Coronavirus.

A ranar Lahadi, an tabbatar da kamuwar mutum 150 da cutar korona yayin da ake jiran sakamakon wasu samfur daga hukumar kula da cutuka masu yaduwa daga Abuja.

Wata majiya ta sanar da SaharaReporters a Katsina cewa, babban birnin jihar da garin Daura ne mace-macen ya fi kamari.

Ya ce wannan ci gaban ya saka zukatan jama'a cikin tsoro saboda babu wanda ya san takamaiman dalilin mace-macen.

"Jama'a na mutuwa, makabartu na cika. Wadanda ke mutuwar da yawansu tsofaffi ne amma suna da wasu cutuka na daban. Muna birne a kalla mutum 12 a rana a maimakon biyu zuwa uku," wani mai hakar kabari a makabartar Danmarna ya sanar da SaharaReporters.

Wasu mazauna garin Daura sun nuna damuwarsu a kan yadda mace-mace ke kara yawa a makonni da suka gabata.

COVID-19: Mace-mace na tada hankulan mazauna birnin Katsina da Daura
COVID-19: Mace-mace na tada hankulan mazauna birnin Katsina da Daura. Hoto daga SaharaReporters
Asali: Twitter

KU KARANTA: Idi: Buhari da gwamnoni sun kulla yarjejeniya biyar a kan bude masallatai

Sun tattauna cewa da yawa daga cikin wadanda ake birnewan tsofaffi ne kuma maza da mata.

Idan zamu tuna, Dr Aminu Yakubu, mutum na farko da ya kamu da cutar a Katsina, ya rasu ne a makonni kalilan da suka gaba.

Hakazalika, Alhaji Umar Farouk Umar, sarkin Daura ya warware daga jinyar cutar inda aka sallamesa daga asibiti.

An gano cewa marigayi likitan kuma mutum na farko da ya kamu da cutar, likitan basaraken ne kuma ya duba matarsa wacce daga baya ta mutu sakamakon cutar.

A wani labari na daban, maginan kabari da masu tsaron makabartu a jihar Kano na cikin wani hali sakamakon ci gaban yaduwar annobar Coronavirus a jihar.

Daily Trust ta gano cewa, tun bayan hauhawar mace-mace a jihar cikin watan da ya gabata, babu wani yunkuri da gwamnatin jihar tayi don bada kariya ga masu karbar gawawwaki don birnewa a makabartu.

Duk da har yanzu ba a alkinta mace-macen da annobar Coronavirus ba, akwai hasashe da kuma manyan alamu da ke danganta mace-macen da cutar.

Wannan ne kuwa yasa aka fara tunanin wadanda ke mu'amala da gawawwakin a gargajiyance.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel