Boko Haram: MNJTF sun ragargaza mayakan ta'addanci ta jiragen yaki

Boko Haram: MNJTF sun ragargaza mayakan ta'addanci ta jiragen yaki

Rundunar sojin hadin guiwa (MNJTF) ta ragargaji mayakan ta'addancin ISWAP a yankunan tsibirin tafkin Chadi, kamar yadda majiya daga rundunar ta sanar.

"Bayan samun bayanan sirri daga majiyoyi daban-daban, mun samu bayanai inda 'yan ta'addan suka rike a Tumbun tare da gano sansani, wurin adana makamai da sauran abubuwan amfanin 'yan ta'addan.

"Dogaro da hakan, dakarun sun kai samame ta jiragen yaki, an ragargaza ababen amfanin 'yan ta'addan," majiyar tace.

Sakamakon samamen ya bayyana cewa an halaka 'yan ta'addan masu tarin yawa tare da kona gine-ginen 'yan ta'addan.

Tashin bama-bamai daga bidiyon ya bayyana cewa an kone ababen hawa da ma'adanar man fetur din 'yan ta'addan.

Hakazalika, jiragen yakin kasar Chadi sun kai samame a Tumbun, shugaban fannin yada labarai na dakarun kasar Chadi, Kanal Timothy Antigha, yace a wata takarda.

Boko Haram: MNJTF sun ragargaza mayakan ta'addanci ta jiragen yaki
Boko Haram: MNJTF sun ragargaza mayakan ta'addanci ta jiragen yaki. Hoto daga HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: An damke malamin da ya yi wa El-Rufai 'wankin babban bargo' a kan hana sallar Idi

Antigha ya kara da cewa: "A kwanaki masu zuwa, dakarun kasar tare da na MNJTF za su tsananta kokarinsu wajen murkushe ragowar 'yan ta'adda.

"Wannan kokari ne don dakile duk wani hari da mayakan ISWAP za su iya kawowa yankin da MNJTF din suke."

A wani labari na daban, rundunar sojin Operation Hadarin Daji ta tarwatsa sansanin 'yan bindiga tare da nasarar halaka a kalla 135 daga cikinsu.

Dakarun sojin saman sun kai samamen ne tsakanin ranar 22 zuwa 23 na watan Mayun 2020 a wurare da dama na maboyar 'yan bindigar da ke jihohin Katsina da Zamfara.

Daga cikin sabon salon kakkabe 'yan bindigar da suka gallabi jama'ar jihohin Katsina da Zamfara, gwamnatin tarayya ta kara tura dakarunta yankin.

A makon da ya gabata ne 'yan bindigar suka saka yankunan a gaba inda suke yi wa jama'a kisan kiyashi tare da kwashe musu Shanunsu.

Bayan kiran da shugabannin yankin tare da masu fadi a ji suka dinga yi wa gwamnatin tarayya, an tura karin sojoji da za su kawo karshen lamarin.

Hakazalika, sojin saman sun kai hari a sansanin Hassan Tagwaye da na Alhaji Auta tare da na Maikomi.

Shugaban dakarun sojin saman Najeriya ya jinjinawa rundunar Operation Hadarin Dajin a kan wannan gagarumar nasarar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel