Kano: Yadda wani bawan Allah ya yanke jiki ya fadi ya mutu bayan gama sallar Idi

Kano: Yadda wani bawan Allah ya yanke jiki ya fadi ya mutu bayan gama sallar Idi

Wani bawan Allah da ba a bayyana sunansa ba ya yanke jiki ya mutu a yayin da ake bikin sallar Idi a unguwar Sharada a jihar Kano.

Vangaurd ta ruwaito cewa mutumin ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu ba da dadewa ba bayan ya gama sallar raka'a biyu na Idi a Kano.

Wata majiya da ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ba ta fadi sunan mutumin ba ta ce mutumin ya fito daga unguwar Kofar Dan Agundi ne domin ya yi sallar Idi a Sharada.

Wani bawan Allah ya yanke jiki ya fadi ya mutu bayan gama sallar Idi a Kano
Wani bawan Allah ya yanke jiki ya fadi ya mutu bayan gama sallar Idi a Kano. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bayan daukar dawainiyar karatunsa, budurwarsa ta kama shi otal da karuwa (Bidiyo)

Acewarsa, "Ba mu san sunanshi ba, ko adireshinsa ko inda ya ke aiki da sauran bayanai.

"Mun dai san daga Kofar Dan Agundi ya taho domin yin salla a Sharada. Ya yanke jiki ya fadi bayan an kammala sallar."

"Yan uwansa da jamian hukumar Hisbah sun dauke gawarsa. Sun koma da shi Kofar Dan Agundi inda aka yi masa jana'iza bisa tsarin koyarwar addinin musulunci," a cewar majiyar.

Musulmi a jihar Kano sun yi bikin salla ne ba tare da shagulgulan da aka saba yi ba a lokacin Sallah a jihar saboda fargabar yaduwar annobar COVID-19 da aka fi sani da coronavirus.

Sallar Idi ke nuna karshen azumin watan Ramadan wadda farali ne ga musulmin da ke fadin duniya inda suke azumtar watar a duk shekara.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa an gudanar da sallar Idi a Kofar Mata da wasu wurare da gwamnati ta bayar da izinin ayi sallar Idi a jihar.

A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar yan sandan jihar Legas ta kama wani Chima da ya bankawa yayarsa mai suna Victoria wuta a gidansu da ke CAC bus stop a Okokomaiko a unguwar Ojo.

Punch Metro ta ruwaito cewa yan uwan biyu suna taya mahaifiyarsu aiki ne a lokacin da ta ke girki nan rikici ya barke tsakanin Victoria da kanin ta Chima.

An gano cewa mahaifiyar tana yi wa jan kunnen Victoria ne a kan kwana a gidan mazaje tunda suka na gida amma sai cacan baki ya kaure tsakaninsu kuma Victoria ta fada wa mahaifiyarta magana mara dadi

Rahoton ya cigaba da cewa munanan kalaman da Victoria ta fada wa mahaifiyarsu ne ya fusata Chima inda ya dako jarkar kalanzir ya buge ta da shi kuma kalanzir din ya zuba a jikinta da mahaifiyar.

Bayan haka sai wuta ta tashi a dakin girkin inda mahaifiyarsu da Victoria suka kone.

Domin ceto su, makwabta sun garzaya da su zuwa wani asibiti a Okokomaiko inda daga nan aka tura Victoria zuwa babban asibitin Igando.

Amma Victoria ta mutu saboda munanan kunan da ta samu yayin da mahaifiyarsu ta samu sauki.

Chima ya yi kokarin tserewa bayan ya lura da abinda ya aikata amma matasan unguwar sun kama shi bayan sun hango hayaki na fitowa daga gidan kuma sun ji ihun wadanda wutar ta yi wa rauni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel