Mutanen gari sun babbaka mutane 12 da suke zarginsu da maita a Cross Rivers

Mutanen gari sun babbaka mutane 12 da suke zarginsu da maita a Cross Rivers

Akalla mutane 12 wanda yawancin su mata ne aka kashe a garin Oku na karamar hukumar Boki ta jahar Cross Rivers sakamakon zarginsu da ake yi maita da tsafe tsafe.

Guardian ta ruwaito mutanen garin sun lakada ma matan dan banzan duka ne, daga bisani kuma suka cinna musu wuta wanda yayi sanadiyyar mutuwar yawanci daga cikinsu.

KU KARANTA: Bikin Sallar wannan shekara na musamman ne - Atiku Abubakar

Sai dai wata majiya da bata bayyana kanta ba ta bayyana cwa wani babban jami’in gwamnatin jahar Cross Rivers ne ya dauki nauyin kashe mutanen.

“An ciro tsofaffin mutanen ne daga gidajensu bayan ana zarginsu da cewa su mayu ne kuma matsafa, daga nan aka cinna musu wuta. Wasu sun mutu, wasu kuma can rai fakwai mutu fakwai, kuma basu samu kulawa ba, hatta a asibitin Okundi.

“Abinda ya sa shi ne, jami’in gwamnatin da ya shirya harin ya yi gargadin kada wanda ya kula tsofaffin, har ma yayi barazanar duk wanda ya kulasu shi ma sai ya sha wahala irin ta su.” Inji majiyar.

Mutanen gari sun babbaka mutane 12 da suke zarginsu da maita a Cross Rivers
Mutanen gari sun babbaka mutane 12 da suke zarginsu da maita a Cross Rivers
Asali: Depositphotos

Daga cikin wadanda aka kashe akwai masu rike da mukaman gargajiya guda 3; Cif Benard Kekong, Edward Kekong da John Otu, dukkaninsu konasu aka ayi.

“Yansandan Okundi sun gagara yin komai saboda dan siyasan ya gargade su da cewa babu ruwansu, yan garin da dama sun tsere don gudun kada mutumin da yaransa su kai musu hari, hatta shugaban garin, Benard Nku ya tsere.” Inji majiyar.

Da aka tuntubi ofishin mashawarcin gwamnan jahar a kan harkar tsari, Sir Alfred Mboto, babban jami’I a ofishin yace sun samu rahoton matasa sun kashe tsofaffi a kan zargin maita.

Duk kokarin da aka yin a jin ta bakin rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar ya ci tura sakamakon ba’a samu kakaakinta, DSP Irene Ugbo a wayar salula ba.

A wani labari, Wani matashi Sadiq Abubakar Ibrahim ya tsinci kansa cikin mawuyacin hali bayan Yansandan babban birnin tarayya Abuja sun harbe shi yayin da yake yin alwala a kofar gida.

Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Mayu a gidansu dake Gwarimpa yayin da Yansandan sanye da kayan gida dauke da bindigogi suka far ma gidan nasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel