Kora daga ofis: Pantami da Dabiri-Erewa sunyi musayar zafafan kalamai

Kora daga ofis: Pantami da Dabiri-Erewa sunyi musayar zafafan kalamai

- Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya musanta cewa ya aike wasu da bindidu su kori ma'aikatan hukumar NIDCOM, daga ofishinsu da ke ginin hukumar NCC

- Pantami ya ce bayyana zargin da shugaban hukumar ta yi na cewa ya bayar da umurnin a fattatki ma'aikatanta a matsayin tsantsagwaron karya

- Hukumar ta NCC kuma ta karyata cewa ta kori maaikatan hukumar da NIDCOM daga wurin da suke aiki a harabar ta

Abike Dabiri-Erewa, shugaban hukumar da ke kula da 'yan Najeriya da ke ci-rani a kasashen waje, NIDCOM, a ranar Lahadi sun yi musayar kalamai da Ministan Sadarwa a kan zargin korar maaikatanta daga ofishinsu.

A yayin da Dabiri-Erewa ta zargi Pantami ta rashin mutunta mata, ministan ya mayar da martani inda ya ce babu gaskiya ko kadan a cikin zargin da ta yi.

Rikicin na su ya samo asali ne bayan tsohuwar yar majalisar a cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin NIDCOM a Twitter ta yi ikirarin cewa antami ya bayar da umurnin korar ma'aikatanta daga ofishinsu na Abuja.

DUBA WANNAN: Bayan daukar dawainiyar karatunsa, budurwarsa ta kama shi otal da karuwa (Bidiyo)

Ta ce hukumar Sadawar ta Najeriya, NCC ce ta basu ofishin kuma har yanzu kayan aikinsu na ciki an rufe bayan wasu mutane da bindigu sun kore su.

A cikin bidiyon ta ce, "Munyi shekara daya bamu da ofis. Ofishin da muka samu, NCC ce ta bamu, Ministan Sadarwa, Mr Isa antami ya kore mu. Cikin kwanaki biyu ya kore mu da bindigu kuma mene ya faru? NCC ce ta bamu wurin.

“Ina birnin Addis-Ababa (kasar Habasha) lokacin da abin ya faru, aka jefa dukkanin ma’aikatana a kan titi dauke da kayan aikinmu, gafaka, da na’urorin daukar hoto duk a watse a kan titi.”

“Abin da ya fi takaici shi ne jami’an tsaron da su ka zo da makamai su ka kore mu daga ofis, sun ce su na aiki ne da umarnin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami.”

A karshe shugabar ta hukumar NIDCOM ta kare jawabinta da cewa: “Na rubuta takarda na yi korafi game da wannan cin mutunci da wani bangaren gwamnati ya yi wa takwaransa.”

A bangarensa, Ministan ya mayar da martani a kan bidiyon da ta fitar inda ya ce Dabiri-Erewa karya ta sharara.

"... Hukumar NCC ne da ke ginin kuma sun karyata abinda ta fadi a dandalin sada zumunta. Minister bai bawa wasu mutane masu bindiga wani umurni ba.

"Ya kamata mu rika fadin gaskiya wurin fitar da rahoto. Ban taba aike wani mai bindiga ba kuma ba ni da kowa."

Pantami ya wallafa sanarwar da kakakin hukumar NCC, Henry Nkemadu ya fitar na karin haske game da batun inda ya ce ba a kori maaikatan NIDCOM daga ofishinsu ba.

Ya ce an samu wasu matsaloli ne saboda ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari zai kai hukumar ta NCC domin kaddamar da wasu ayyuka.

"Domin tabbatar da tsaro a kan tantace mutane kafin ziyarar shugaban kasar, a lokacin ziyarar da bayan ta tafi. Sanannun mutane kadai ake bari su shiga harabar ginin.

"Don haka ba zai yiwu Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Ibrahim Pantami ya aike mutane dauke da bindigu su kori jamian hukumar NIDCOM daga ginin hukumar NCC ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel