Bikin Sallar wannan shekara na musamman ne - Atiku Abubakar

Bikin Sallar wannan shekara na musamman ne - Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar, ya taya Musulmin Najeriya da na sauran sassan duniya bikin murnar karamar Sallah.

Kazalika, ya taya Musulmi juyayin yin bikin Sallah a cikin sabon yanayi, sabanin yadda su ka saba yin Sallar Idi cikin jama'a da farin ciki da walwala.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Atiku ya ce, "annobar korona jarrabawa ce daga Allah, a yayin da mu ka kammala watan azumin watan Ramada, kar mu manta cewa addininmu ya horemu da kare rayuka da kuma yin biyayya ga dokokin hukuma, musamman a lokaci irin wannan."

Atiku ya yi kira ga shugabanni su nuna sadaukarwa tare da yi musu tunin cewa wannan lokaci ne da ya kamata su jingine rayuwar kawa da jin dadi domin nuna tausayawa ga jama'a.

Kazalika, ya bukaci shugabanni a fadin duniya su kasance ma su koyi da kyawawan halaye irin na Annabi Muhammad (SAW) da sauran halifofinsa da su ka nuna sadaukarwa yayin da su ke rike da shugabanci.

Bikin Sallar wannan shekara na musamman ne - Atiku Abubakar
Atiku Abubakar
Asali: Twitter

"Alhakin gwamnati ne a kowanne mataki ta tsarawa jama'arta hanyoyin da za su murmure a yayin da ake fita daga kuncin annobar cutar korona," a cewar Atiku.

DUBA WANNAN: Kotu ta hana malamin addinin Musulunci auren matashiya mai shekaru 16

A karshe, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su guji cushewar jama'a a wuri guda tare da yawan wanke hannaye da sabulu da biyayya ga sauran matakan kare kai da dakile yaduwar kwayar cutar korona.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel