Sojoji sun kama injin nika da makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram

Sojoji sun kama injin nika da makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram

A cigaba da yaki da ta'addanci a jihar Borno, bataliyar sojojin rukuni na 7 a rundunar soji ta daya a atisayen ofireshon LAFIYA DOLE (OPLD) ta samu nasarar kai wasu hare - haren kwanton bauna a kan mayakan kungiyar Boko Haram da na takwararta ISWAP.

Dakarun soji na cigaba da kaddamar da manyan hare - hare tare da samun galaba a kan 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram da ISWAP a karkashin atisayen KANTANA JIMLAN wanda shugaban rundunar soji, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya kaddamar domin tsananta yaki da 'yan ta'addar.

A irin wadannan zafafan hare - haren da dakarun soji ke kaiwa, sun kai wani hari a wata maboyar 'yan ta'adda da ke kan hanyar zuwa Adzunge.

Ba a kama kowa ba yayin harin saboda 'yan ta'addar sun tsere bayan sun hango rundunar sojoji ta tunkaro kauyen.

Sojojin sun samu kayan amfanin 'yan ta'addar da su ka hada da babur guda biyu da wani babban injin nika nikan lausi, wanda aka fi sani da 'Lister'

A ranar 13 ga watan Mayu a yankin Pulka, rundunar soji ta kai harin kwanton bauna a kan wasu mayakan kungiyar Boko Haram a yayin da su ke gudun hijira daga dajin Sambisa zuwa tsaunin Mandara.

Dakarun soji sun kashe biyar daga cikin 'yan ta'addar sannan sun samu bindigu kirar AK47 guda uku, wata jaka mai dauke da kakin 'yan kungiyar Boko Haram da sauran wasu alburusai bayan na cikin bindigun da aka kama.

DUBA WANNAN: Hotunan yadda El-Rufa'i ya kafa ya tsare a kan iyaka don hana Kanawa shiga Kaduna

Sojoji sun mayar da martani da karfinsu yayin wani harin kwanton bauna da 'yan Boko Haram su ka kai mu su a kauyen Gajigana a ranar 18 ga watan Mayu.

Kokarin mayakan na guduwa, bayan sun kwashi kashinsu a hannu, bai yi nasara ba, saboda sojojin da aka turo kawo agaji sun yi zafin nama wajen datsesu a hanya da kuma kama makaman da ke tare da su.

Makaman sun hada da bindigun AK47 guda biyu, alburusai, gurneti da bam samfurin LG3.

Sojoji sun kama injin nika da makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram
Sojoji sun kama makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram
Asali: Facebook

Sojoji sun kama injin nika da makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram
Sojoji sun kama injin nika da makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram
Asali: Facebook

Sojoji sun kama injin nika da makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram
Sojoji sun kama injin nika da makamai bayan sun kashe dumbin yan Boko Haram
Asali: Facebook

Kazalika, a ranar 19 ga watan Mayu, sojojin da ke aiki a Dikwa sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram guda biyu tare da raunata sauran da su ka kai mu su hari tare a sansaninsu da ke yankin Boboshe.

Buratai ya nuna jin dadinsa a kan nasarorin da dakarun rundunar su ka samu tare da hadin gwuiwar matasa 'yan sa kai.

Bayan haka, ya bukaci kwamandan rundunar ya rubanya irin wannan namijin kokari domin a samu kawo karshen makiyan kasa cikin gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: