Allah ya yi wa sarki mai shekara 141 rasuwa a Najeriya

Allah ya yi wa sarki mai shekara 141 rasuwa a Najeriya

Mai martaba Onilua na IIua, a karamar hukumar Kajola na jihar Oyo, Obas Samuel Afolabi ya rasu.

Oba Afolabi, da ake kyautata zaton shine sarkin da ya fi sauran sarakuna tsufa a jihar Oyo ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis bayan fama da gajeruwar rashin lafiya mai nasaba da tsufa.

An ce shekarunsa 141 a duniya lokacin da ya rasu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewar majiyar, an haifi marigayi sarkin ne a garin IIua a shekarar 1879 kuma an nada shi sarki a garin shekaru 38 da suka shude yana da shekara 102 a duniya.

Sarki mai shekaru 141 ya rasu a Najeriya
Sarki mai shekaru 141 ya rasu a Najeriya. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

Marigayin sarkin manomi ne a garin Arigidana, Baba Ode a karamar hukumar Itseiwaju da ke jihar ta Oyo kafin a nada shi sarki.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa muka yi Sallar Idi a ranar Asabar – Sheikh Lukuwa

An nada shi sarki ne a shekarar 1981 bayan rasuwar Oba Majaro.

An gano cewa dukkan masu nadin sarki da mutanen gari sun amince da nadin Afolabi a matsayin sarki a lokacin a garin na IIua.

A wani labarin, kun ji cewa Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta kashe wasu fitinannun 'yan bindiga takwas da suka dade suna gallabar yankin kuma ake ta nemansu tun watannin da suka gabata.

An kashe 'yan bindigar ne a karamar hukumar Bali ta jihar bayan bayanan sirrin da aka samu a kan maboyarsu.

Sun kware a yin garkuwa da jama'ar yankin tare da karbar kudin fansa, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, David Misal ne ya sanar da hakan bayan ya ga gawawwakin masu garkuwa da mutanen a ranar Juma'a.

Kamar yadda Misal ya tabbatar, bayan 'yan bindiga sun hango jami'an tsaron sai suka bude musu wuta tare da musayar harsasai.

Hakan ne ya yi sanadiyyar mutuwarsu kuma an samo harsasai, bindigogin da kuma kayan sojoji.

Misal ya ja kunnen duk wani dan ta'adda a yankin da ya tuba ko kuma ya mika kanshi, idan ba haka ba zai fuskanci fushin hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel