Korona: Karin mutum 265 sun kamu a Najeriya, jimilla 7526

Korona: Karin mutum 265 sun kamu a Najeriya, jimilla 7526

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 265 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.51 na daren ranar Asabar, 23 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 365 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

133-Lagos

34-Oyo

28-Edo

23-Ogun

22-FCT

6-Plateau

5-Kaduna

3-Borno

3-Niger

2-Kwara

2-Bauchi

2-Anambra

2-Enugu

DUBA WANNAN: Bayan daukar dawainiyar karatunsa, budurwarsa ta kama shi otal da karuwa (Bidiyo)

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar 23 ga watan Mayun 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 7526.

An sallami mutum 2174 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 221.

A wani labarin, kun ji cewa hukumar gyaran hali ta jihar Kaduna ta ki karbar wani sabon fursuna da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta kawo mata.

Sanusi Danmusa, shugaban gidan gyaran halin, a ranar Jumaa ya ce an ki karbar sabon fursunan ne saboda kare wadanda ke gidan gyaran halin daga kamu da COVID-19.

Ya ce gidan gyaran halin ta dena karbar sabbin wadanda aka yanke wa hukunci har ma da masu ziyara saboda bullar annobar ta coronavirus.

An yanke wa Sadiq Musa, mai sanaar canjin kudi hukucin zaman shekaru bakwai a gidan gyaran hali ba tare da zabin biyan tara ba.

Da ya ke tsokaci a kan rashin karbar fursunan, shugaban hukumar EFCC na Kaduna, Yakubu Mailafia ya ce bai san inda hukumar gidan gyran halin ta ke so ya kai wanda aka yanke wa hukuncin ba.

Ya ce, "Hukumar EFCC tana da kaida game da tsare masu laifi kuma gidan gyaran hali shi ne wuri na karshe da ake kai wadanda aka yanke wa hukunci, ina za mu kai su?"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel