Jajiberin Idi: Ganduje ya bai wa Limamai muhimmiyar sanarwa

Jajiberin Idi: Ganduje ya bai wa Limamai muhimmiyar sanarwa

Gwamna Umar Ganduje na jihar Kano ya shawarci malaman addinin islama a jihar da su gabatar da gajeriyar huduba yayin sallar idi wacce ya aminta da a yi duk da gwamnatin tarayya ta soki hakan.

A wata takarda da sakataren yada labaran gwamnan ya fitar a ranar Asabar, Abba Anwar ya ce za a yi sallar idi a kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Ya ce dole ne Musulmi su kiyaye dokokin da hukumomin lafiya suka tanadar don sallar jam'i.

"Kamar yadda manyan Malamai suka shawarci limamanmu, ya kamata a yi huduba gajera a yayin sallar Idin saboda kalubalen COVID-19 da muke fuskanta.

"Akwai bukatar jama'a su hanzarta watsewa ana kammala sallar sannan su ci gaba da kiyaye dokokin kiwon lafiya," yace a takardar.

Jajiberin Idi: Ganduje ya bai wa Limamai muhimmiyar sanarwa
Jajiberin Idi: Ganduje ya bai wa Limamai muhimmiyar sanarwa. Hoto daga The Cable
Asali: Facebook

KU KARANTA: Kano: Ganduje ya dauka tsatsauran mataki a kan karin farashin kayayyaki

A wani labari na daban, a jihar Kano da sauran jihohin yankin Arewacin Najeriya, masu saida kayayyaki na ganin watan azumi a lokacin da suke tara riba da yawa. Su kan kara kudin kayayyakin ba kamar yadda suka saba siyarwa ba.

Duk da jama'a da malamai na iyakar kokarinsu wajen ganin an wa'azantar da 'yan kasuwar a kan illar hakan, suna ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Ba zato, sai 'yan kasuwar suka fara amfani da kullen COVID-19 wajen kara farashin kayayyakin bukata ta yadda farashin ya kazanta. Lamarin ya kai ga an samu karin farashin da kashi 200 a cikin kwanaki kalilan.

A saboda haka, hankalin jama'a ya tashi don ba kowa ke iya cin abinci ba. Jama'ar jihar sun yi kira ga gwamnati da su tallafa musu don shawo kan wannan matsala, jaridar Daily Trust ta wallafa.

A yayin martani a kan wannan koken, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar yaki da rashawa ta jihar da ta dauka matakan da suka dace.

A yayin aiki a kan umarnin, shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya fitar da hanyoyin daidaita farashin kayayyaki a jihar.

A ranar farko da aka fara binciken, an garkame wuraren adana kayayyaki masu tarin yawa. An gano cewa 'yan kasuwar ke boye kayayyaki wadanda aka bankado daga baya.

Daga baya, Gado ya yi taro da kungiyar 'yan kasuwa ta jihar sannan suka samu matsaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel