Na kashe dan uwan na saboda mahaifin mu nuna masa kauna - Wanda ake zargi da kisa

Na kashe dan uwan na saboda mahaifin mu nuna masa kauna - Wanda ake zargi da kisa

'Yan sanda na musamman na IRT karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan dan sanda (DCP) Abba Kyari, sun kama wani matashi Ibrahim Abdullahi (20) da Hassan Amadu (22) kan kisar Kadade Abdullahi na kauyen Amana Maikasuwa a Kaduna.

An kama wanda ake zargin mai shakaru 20 bayan jamian IRT da ke aiki da Operation Puff Adder, na Kateri sun kama daya daga cikin yan kungiyar barayin shanun da suka kashe Kadede.

Bayan yan sanda sun kama shi tare da yi masa tambayoyi, Ibrahim ya amsa cewa yana cikin wata kungiya da suka kware wurin satar shanu, fashi da makami da garkuwa da mutane.

Ya kuma bayyana cewa shine ya kitsa yadda aka kashe yayansa saboda mahaifinsu ya fi kaunarsa.

Na kashe dan uwan na saboda mahaifin mu ya ci son shi - Wanda ake zargi da kisa
Na kashe dan uwan na saboda mahaifin mu ya ci son shi - Wanda ake zargi da kisa. Hoto daga LIB
Asali: UGC

Ibrahim ya ce:

"Mahaifinmu yana da mata hudu da yara masu yawa. Ban san abinda ya gani a jikin Kadede ba da babu yadda zai yi wa wani daga cikin yayansa wani abu ba tare da yi mana misali da Kadade ba.

"An tura ni makarantar arabiyya a Kaduna, shi kuma Kadede ya tafi makarantar frimari da sakandare. Mahaifinmu ya ce ba dole ne dukkanmu mu tafi makaranta ba don yana son dukkanmu mu zama manoma.

"Amma duk da haka, da ya samu dama sai ya fara mana gori cewa mu jahilai ne yana cewa ba mu iya turanci ba.

"Ta yaya zan koya turanci tunda mahaifi na bai tura ni makarantar boko ba? Noma da kiwo kawai na iya. Ta kai ga har sai da na yi aure don in nuna masa na yi hankali.

"Bayan na yi aure, mahaifinmu ya bani shanu 20 da filaye biyu. Dalilin da yasa ni da yan kungiya ta muka kashe dan uwa na shine mahaifinmu ya fi yarda da shi.

"Na kashe shi ne saboda Naira miliyan 1.7 da mahaifinmu ya samu bayan sayar da shanu ya kuma bawa dan uwa na kudin ya ajiye.

"Dan uwa na ne aka bawa shanun ya sayar ya samu miliyan 1.7 kuma ya rika cika baki. Mahaifinmu yana ta murna kan lamarin kuma ya ce masa ya ajiye kudin a hannunsa.

"Muna tsamanin zai raba kudin tare da mu. Wata rana bani da kudi sai na tambayi mahaifinmu ya bani kudi. Ya fara zagi na yana cewa in rika koyi da Kadede.

"Abin ya bata min rai sosai sai na kira dan kungiyan mu, Haruna, na fada masa akwai kudi a gidanmu. Na fada musu su tabbatar sun kashe kani na.

"Duk da cewa na yi nadamar abinda na aikata, nayi tsamanin mahaifinmu zai bari in fara kulawa da kudadensa. Mahaifina ya shiga damuwa sosai amma na bashi hakuri na fada masa kaddara ce daga Allah.

"Da safe, na tafi daji na hadu da su kuma sun fada min N300,000 suka samu a hannun dan uwa na. Na karba N100,000 su kuma suka raba sauran."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel