Bayan daukar dawainiyar karatunsa, budurwarsa ta kama shi otal da karuwa (Bidiyo)

Bayan daukar dawainiyar karatunsa, budurwarsa ta kama shi otal da karuwa (Bidiyo)

- Bidiyon wata budurwa na shan mugun dambe da saurayinta tare da karuwarsa ya jawo cece-kuce

- A bidiyon an ga budurwar na shan mugun dambe da saurayinta inda wasu ke rirriketa don hana ta

- Budurwar ta yi ikirarin cewa ta dauka nauyin dukkan karatunsa amma sai ta kama shi da wata a otal

Wata budurwa 'yar Najeriya ta kama saurayinta da mugun dambe a tsakar titi bayan ta kama shi dumu-dumu da wata yana cin amanarta.

Kamar yadda bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani ya bayyana, budurwar ta kashe makuden kudi a kan saurayin wanda a da bashi da komai.

Budurwar ta ce ita ke kula da shi na tsawon shekaru uku, amma a yau ta kama shi dumu-dumu da karuwa a otal.

Wannan abu da ta bankado kuwa ya matukar fusata ta domin hakan yasa ta ja shi da dambe a titi.

Ba wannan bane karo na farko da ake fuskantar cin amana daga bangaren mata ko maza ba a soyayya.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kwace kauyuka a Sokoto, sun nada sabbin alkalai - Sanata Gobir

Ga bidiyon a kasa.

A wani labari na daban, dan majalisar tarayya mai wakiltar yankin Sokoto na gabas a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Gobir, ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga sun kwace wani sashi na mazabarsa.

A wata tattaunawar da yayi da jaridar The Punch a Abuja ranar Juma'a, Gobir ya jajanta yadda 'yan ta'adda suka tsige sarakunan gargajiya da na siyasa a wasu kauyuka tare da nada nasu.

Kamar yadda dan majalisar APC din ya bayyana, wadanda kauyukansu ke da kusanci da iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar suna samun zaman lafiya saboda dakarun sojin kasar Nijar da ke basu kariya.

Dan majalisar yace, "Babban kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu shine yadda 'yan bindiga ke kwace mana kauyuka da rana tsaka.

"Sun nada kansu a matsayin alkalai. Sun tsige sarakunan gargajiya da na siyasa, don haka su ke mulki.

"A halin yanzu 'yan bindigar ne ke sasanci a tsakanin jama'a idan an samu rashin jituwa. Su ke sasanta fada tsakanin mata da miji da sauransu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel