El–Rufai ya sake komawa iyaka ya kafa ya tsare don hana Kanawa shiga Kaduna (Hotuna)

El–Rufai ya sake komawa iyaka ya kafa ya tsare don hana Kanawa shiga Kaduna (Hotuna)

A yau, Asabar 23 ga watan Mayu, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya sake jagoranci tawagar jami'an gwamnatinsa domin tabbatar da dokar hana shige da fice a tsakanin jihohi.

A jiya, Juma'a gwamnan tare da tawagansa sun fita irin wannan aikin domin tabbatar da cewa babu wani matafiyi da ya ketare iyakar jihar ya shigo ba tare da kwakwaran dalili na aiki ko doka ba.

Mutane da dama kan yi balaguro daga birane daban daban a jajiberin sallah domin zuwa gida yin bikin sallah tare da iyalansu da sauran yan uwa da abokan arziki.

A kwanan baya dai wata bidiyo ta rika yawo a dandalin sada zumunta inda gwamnan ke koka wa kan yadda almajiran Kaduna da aka dawo da su daga Kano mafi yawancinsu ke dauke da cutar korona.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kwace kauyuka a Sokoto, sun nada sabbin alkalai - Sanata Gobir

Gwamnan ya nuna cewa an saka dokar hana fice da shige tsakanin jihohin ne domin kiyayye lafiyar alumma amma wasu hukumomin tsaro na karbar kudi suna barin mutane na shiga Kaduna.

Hakan yasa gwamnan ya dau alwashin cewa zai tafi iyakar jiharsa da Kano da kansa ya tabbatar ana biyayya ga dokar ta hana shige da fice musamman a wannan lokaci da sallah ta karato.

Gwamnan Kadunan ya wallafa hotuna a shafin gwamnatin jihar na Twitter @GovKaduna

A wani labarin, kun ji cewa hukumar gyaran hali ta jihar Kaduna ta ki karbar wani sabon fursuna da Hukumar Yaki da Rashawa ta EFCC ta kawo mata.

Sanusi Danmusa, shugaban gidan gyaran halin, a ranar Jumaa ya ce an ki karbar sabon fursunan ne saboda kare wadanda ke gidan gyaran halin daga kamu da COVID-19.

Ya ce gidan gyaran halin ta dena karbar sabbin wadanda aka yanke wa hukunci har ma da masu ziyara saboda bullar annobar ta coronavirus.

An yanke wa Sadiq Musa, mai sanaar canjin kudi hukucin zaman shekaru bakwai a gidan gyaran hali ba tare da zabin biyan tara ba.

Da ya ke tsokaci a kan rashin karbar fursunan, shugaban hukumar EFCC na Kaduna, Yakubu Mailafia ya ce bai san inda hukumar gidan gyran halin ta ke so ya kai wanda aka yanke wa hukuncin ba.

Ya ce, "Hukumar EFCC tana da kaida game da tsare masu laifi kuma gidan gyaran hali shi ne wuri na karshe da ake kai wadanda aka yanke wa hukunci, ina za mu kai su?"

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel