Annobar COVID-19 jarrabawa ce daga Allah, in ji Atiku

Annobar COVID-19 jarrabawa ce daga Allah, in ji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya ce annobar COVID-19 gwaji ne daga Allah.

A cikin sakonsa na Sallah da ya fitar a ranar Asabar, Atiku ya yi kira ga yan Najeriya su cigaba da bin dokokin da hukumomin lafiya suka bayar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce hukumomin sun bayar da dokokin ne domin amfanin 'yan Najeriya da sauran mutane a duniya.

COVID-19 jarrabawa ce daga Allah, in ji Atiku
COVID-19 jarrabawa ce daga Allah, in ji Atiku. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda hukumar gidan gyaran hali ta Kaduna ta ki karbar fursuna saboda fargabar korona

Atiku ya ce, "Dukkan wadannan matakan ba za su rage wani abu cikin azumin mu ba, domin mu musulmi mun yarda cewa duk abinda ya faru kaddara ce daga Allah.

"Alkurani da hadisan manzon mu Annabi Muhammad SAW sun koyar da mu cewa Allah zai gwada imaninmu."

"Annobar COVID-19 da muka fama da shi gwaji ne daga Allah saboda haka bayan yin azumi a matsayin mu na musulmi, mu cigaba da tunawa cewa wannan na cikin gwajin da Allah ya ke mana kuma mu cigaba da bin umurnin hukumomi musamman a lokacin irin wannan.

"Umurnin gujewa taron mutane, yin nesa-nesa da juna, wanke hannu lokaci zuwa lokaci an saka su ne don amfanin mu da sauran al'umma.

"A matsayin mu na musulmi, nauyi ya rataya a kan mu na yin aiki da addua domin ganin wannan annobar ta gushe a duniya nan ba da dadewa ba."

Atiku ya ce ya zama dole gwamnatoci a dukkan matakai su bawa walwala da jin dadin mutanensu muhimmanci a lokacin da suke shirin yadda za a gudanar tsari bayan korona.

"Dukkan mutane da ke rike da madafin iko a duniya su koyi darasi kan yadda Manzon Allah SAW da sahabansa suka bawa jin dadin mutane muhimmanci lokacin da suke jagorancin," in ji shi.

"Yanzu lokaci ne na sadaukarwa. Ba lokacin barna bane da rayuwa da jin dadi. Bikin sallar Idi na bana ya fita daban da saura.

"Amma ina yi wa musulmin Najeriya da na sauran kashen duniya fatar yin bikin sallah a lokacin da muka addu'a tare da iyalan mu."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel