COVID-19: Ta yuwu masu hakar kabari a Kano, suna haka nasu ne

COVID-19: Ta yuwu masu hakar kabari a Kano, suna haka nasu ne

Maginan kabari da masu tsaron makabartu a jihar Kano na cikin wani hali sakamakon ci gaban yaduwar annobar Coronavirus a jihar.

Daily Trust ta gano cewa, tun bayan hauhawar mace-mace a jihar cikin watan da ya gabata, babu wani yunkuri da gwamnatin jihar tayi don bada kariya ga masu karbar gawawwaki don birnewa a makabartu.

Duk da har yanzu ba a alkinta mace-macen da annobar Coronavirus ba, akwai hasashe da kuma manyan alamu da ke danganta mace-macen da cutar.

Wannan ne kuwa yasa aka fara tunanin wadanda ke mu'amala da gawawwakin a gargajiyance.

Wannan tsoron ya biyo bayan rashin sanin takamaiman abinda ya kashe mamatan jihar.

Daily Trust ta gano cewa, tun bayan da jihar Kano ta fara kirga mace-mace sakamakon annobar, ba a san inda ake birne mamatan ba wanda hakan yasa ake zargin ko makabartun gargajiya ake kaisu.

A jiya Juma'a kadai, mutum 36 ne suka rasa rayukansu sakamakon annobar a jihar Kano, kuma babu wani gamsasshen bayani game da mamatan da kuma inda ake birne su.

Alhaji Sheriff Hadi Kabir, shugaban kwamitin makabartar Fagge, ya jaddada bukatar samar wa masu hakar kabari kayayyakin kariya.

Ya ce tunda ba a san abinda ya kashe wasu daga ciki ba, kamata yayi a mika kayayyakin kariya tare da horar da masu hakar kabari yadda za su gujewa kamuwa da cutar yayin da suke aikin sa kai.

COVID-19: Ta yuwu masu hakar kabari a Kano, suna haka nasu ne
COVID-19: Ta yuwu masu hakar kabari a Kano, suna haka nasu ne. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaza 'yan ta'adda 135 a Katsina da Zamfara

A wani labari na daban, Sheikh Bello yabo dan asalin jihar Sokoto ya shiga hannun jami'an tsaro tun bayan bazuwar bidiyon da ya caccaki gwamnan Kaduna a kan hana sallar Idi.

A wani sautin murya mai tsayin kusan minti biyar, malamin addinin Islama mai suna Sheikh Bello Yabo, ya caccaki Gwamna Malam Nasir El-Rufai saboda hana sallar Idi da yayi a jihar Kaduna.

A sautin muryar, ya yi kira ga Musulmi da su bijirewa hukumomi a kowanne gari da aka hana su fita sallar Idin karamar sallar don dakile yaduwar cutar korona, kamar yadda jaridar SaharaReporters ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel